An gurfanar da wani mutum a gaban kotu bisa kan sace yar’uwarsa a Kaduna

An gurfanar da wani mutum a gaban kotu bisa kan sace yar’uwarsa a Kaduna

  • An gurfanar da wani mutum mai suna Abubakar Haliru a gaban wata babbar kotun Kaduna bisa zargin yin garkuwa da yar'uwarsa
  • Haliru tare da wasu mutum biyu Nuhu Ibrahim da Rashidu Ibrahim sun yi tarayya wajen garkuwa da wata Hajiya Binta Mohammed
  • Da farko dai an bayar da belin wanda ake zargin saboda rashin lafiya amma sai aka sake kama shi bayan mutanen gari sun gudanar da zanga-zanga

Kaduna - Wata babbar kotun jihar Kaduna da ke Dogarawa, Zaria ta gurfanar da wani mutum mai suna Abubakar Haliru na Magume da wani Nuhu Ibrahim da Rashidu Ibrahim kan zargin garkuwa da wata Hajiya Binta Mohammed.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a shekarar bara cewa hedkwatar rundunar yan sanda a Abuja ta gurfanar da wasu mutane 48 bisa zargin garkuwa da mutane, kisa da sauransu.

Kara karanta wannan

An kuma: 'Yan bindiga sun sake yin awon gaba da jami'in kwalejin Zamfara

Abubakar Haliru wanda ya kitsa garkuwa da yar'uwarsa, Binta Mohammed na daga cikin mutum 48 da aka gurfanar, bayan ya gaza biyanta kudin da ya ranta domin habbaka kasuwancinsa na noma.

An gurfanar da wani mutum a gaban kotu bisa kan sace yar’uwarsa a Kaduna
An gurfanar da wani mutum a gaban kotu bisa kan sace yar’uwarsa a Kaduna Hoto: Thisday
Asali: UGC

An sake kama Haliru wanda aka baiwa beli saboda rashin lafiya sannan aka tsare shi a gidan gyara hali bayan mazauna garin Magume sun yi zanga-zanga a Zaria.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma a zaman da aka sake gurfanar da shi a ranar Laraba, Lauyan masu shigar da kara Tanko Mohammed, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara na farko (Abubakar Haliru) ne kawai ke gaban kotu yayin da Nuhu Ibrahim da Rashidu Ibrahim ke tsare.

A bisa tuhumar da ake masa, laifin Haliru ya ci karo da sashe na 246 na dokar Penal Code na jihar Kaduna.

Sai dai wanda ake zargin ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi sannan lauyan mai gabatar da kara ya nemi a ba shi ranar da zai gabatar da shaidu.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Shehu Sani ya bayyana matsayinsa a kan tsarin mulkin karba-karba

Lauyan mai kara ya kuma ya fada ma kotu cewa an kammala bincike kan lamarin kuma sun shirya ma shari'ar, inda ya bayyana cewa suna da shaidu hudu da za su kira.

Lauyan da ke kare wanda ake kara, Mista Isa Shuaibu, ya fada ma kotu cewa ya gabatar da takardar neman beli amma mai sharia, Justis Kabir Dabo, ya ce kotun ba za ta iya bayar da irin wannan bukata ba har sai ta tantance yadda shaidu da kuma yadda shari’ar ke tafiya.

Don haka ya ba da damar ci gaba da sauraren karar sannan ya dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranakun 24 da 25 ga watan Janairu, rahoton Pulse.

Dabo ya kuma umurci jami’an hukumar gyara hali ta Najeriya da su kai wanda ake kara zuwa cibiyar lafiya domin samun kulawar likitoci.

Dubu ta cika: Wani mutum ya shiga hannu yayin da ya kashe yaransa uku ya adana gawarwakinsu a cikin firinji

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun tafka barna a Zariya, sun kashe mutane sun saci dabbobi

A wani labarin, rundunar yan sanda a jihar Enugu ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ifeanyi Amadikwa kan zargin kashe yaransa da kuma adana gawarwakinsu a cikin firinji.

Hukumar yan sandan ta ce wanda ake zargin shi ne mahaifin biyu daga cikin yaran sannan ta ukun kuma 'yar matarsa ce.

Rundunar ta kuma ce mahaifiyar yaran ta barsu a karkashin kulawar wanda ake zargin a ranar 4 ga watan Janairu, inda ita kuma ta tafi kasuwa, The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng