Har yanzu Yan Boko Haram ne suke da iko kan wasu kananan Hukumomi a Borno, Gwamna Zulum
- Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya magantu a kan kasancewar yan ta'addan Boko Haram a wasu yankunan jihar
- Zulum ya ce har yanzu kananan hukumomi biyu na Abadam da Guzamala na a karkashin ikon Boko Haram
- Ya kuma nuna damuwa kan yadda yan ta'addan ISWAP ke ci gaba da karuwa a yankin Kudancin Borno
Borno - Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya bayyana cewa har yanzu kananan hukumomi biyu na Abadam da Guzamala da ke jihar na karkashin ikon Boko Haram.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da kwamitin majalisar dattawa kan rundunar soji, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati, Maiduguri a ranar Laraba, 12 ga watan Janairu, Daily Trust ta rahoto.
Zulum ya nuna damuwa kan yadda yan ta'addan kungiyar ta ISWAP ke ci gaba da karuwa a yankin Kudancin Borno, rahoton Vanguard.
Zulum ya ce:
"Ya zama dole na jinjinawa rundunar sojin Najeriya kan zaman lafiya da aka samu a yankunan jihar da dama amma zan roki rundunar da ta dauki matakin yaki da yan ta'adda sannan ta kakkabe su saboda a halin yanzu ISWAP na daukar mayaka a wasu yankunan jihar.
"Idan ba a yi komai don dubawa da magance karuwar mayakan ISWAP wadanda ke da makamai da kayan aiki masu karfi da hatsari sannan suke samun kudi fiye da Boko Haram ba, hakan zai zama bala’i ba ga jihar Borno kadai ba, har ma ga kasa baki daya. Suna kara habbaka kuma magance wadannan matsalolin ba mai wahala bane a gare mu; muna bukatar fatattakar ISWAP a wannan mataki na farko.
“Mayakan ISWAP suna hawa shingayen binciken ababen hawa a tsakanin Damboa da Biu, suna karbar haraji daga hannun jama'a saboda a kwanaki uku da suka wuce, na samu bayanin tsaro cewa sun gudanar da wani biki da mashina sama da 300. Akwai bukatar a yi wani abu musamman a yankunan Askira, Chibok da Damboa.
"Wani batu kuma shine cewa hedkwatar kananan hukumomin biyu na a karkashin ikon yan ta'addan Boko Haram har yanzu, Malamfatori a karamar hukumar Abadam da Guzamala. Muna son masu wadannan kananan hukumomi biyu su karbi mulki, wato gwamnatin jihar Borno da na kananan hukumomin biyu.
"Na jinjinawa sojojin Najeriya kan samun zaman lafiya a yankunan jihar da dama kuma babu laifi idan na nemi su farka daga barcin da suke yi wajen magance matsalolin ISWAP."
Borno: 'Yan ISWAP sun kai hari Cibiyar Yaƙi da Zaman Lafiya na Buratai, Sun halaka mutane sun ƙona motocci
A wani labarin, a kalla mutane biyu ne su ka rasa rayukansu sakamakon farmakin da mayakan ISWAP suka kai Cibiyar Tukur Yusuf Buratai ta yaki da kuma samar da zaman lafiya, TBI, da ke Jami’ar Sojin Najeriya wacce take kauyen Buratai a karamar hukumar Biu.
Buratai shi ne asalin kauyen tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya ta kasa, kuma yanzu haka jakadan Najeriya ne a Jamhuriyar Benin, Tukur Buratai.
Asali: Legit.ng