‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan jarida, Salisu Maki, a Nasarawa

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan jarida, Salisu Maki, a Nasarawa

  • Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan jarida mai aiki da Nasarawa Broadcasting Service, Salisu Maki a Lafia, babban birnin jihar
  • Sun sace Maki ne da misalin karfe 9 na safiyar ranar Talata a kan titin Akurba da ke karamar hukumar Lafia bayan komawarsa gida daga wurin aiki
  • Ganau sun shaida yadda ‘yan bindigan su ka isa har harabar gidan su na harbi ko ta ina wanda hakan ya ja jama’an gari su ka tsere daga nan su ka sace shi

Nasarawa - Wasu ‘yan bindiga wadanda sun kai 9 a ranar Talata, sun yi garkuwa da wani dan jarida wanda ma’aikaci ne da Nasarawa Broadcasting Service, Salisu Maki a Lafia, babban birnin jihar, Vanguard ta ruwaito.

Sun sace Maki ne da misalin karfe 9:30 na safiyar Talata a gidansa da ke kan titin Akurba a karamar hukumar Lafia yayin da ya ke hanyarsa ta komawa gida daga aiki.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun tafka mummunar barna

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan jarida, Salisu Maki, a Nasarawa
'Yan bindiga sun sace dan jarida, Salisu Maki, a Lafia. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ganau sun shaida yadda ‘yan bindigan su ka afka har wuraren gidan Maki su na harbe-harbe inda su ka tsorata jama’a daga nan su ka yi garkuwa da mutumin.

Har gida suka bi shi

Vanguard ta bayyana yadda makwabcin Mr Maki ya ce an yi garkuwa da shi ne bayan ya isa gida daga ofishinsa inda ya yi aikin dare.

Kamar yadda ganau din ya shaida:

“Lokacin da mutumin ya isa gida daga wurin aiki, ‘yan bindiga sun afka harabar gidansa su na harbe-harbe daga nan su ka sunkuce shi suka tsere.”

Kakakin ‘yan sandan jihar ya ce ana kokarin ceto shi

Jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, ASP Raham Nansel ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kakakin ya ce kwamishinan ‘yan sanda ya tura rundunoni daban-daban don binciko ‘yan bindigan da kuma ceto dan jaridan.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Yadda jami'an DSS 5 suka taimaka min na yi garkuwa da kwastoma na, Wanda ake Zargi

A wani labarin, kun ji cewa wani Akeem Ogunnubi mai shekaru 42 ya bayyana yadda ya yi garkuwa da wani dan kasuwa a Sabo mai suna Bola cikin ranakun karshen mako, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olawale Olokode dama ya bayar da labari yayin tasa keyar mutumin da ake zargi cewa wasu maza dauke da bindigogi sun sace wani dan canji har cikin ofishinsa a ranar 30 ga watan Disamban 2021 da misalin karfe 5:30 da yamma.

Wanda lamarin ya faru da shi kamar yadda Olukode ya shaida ya ce sun zarce da shi daji ne sannan suka bukaci kudin fansa kafin su sake shi, a nan su ka yi masa kwacen N204,000 sannan suka tsere suka bar shi a wurin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bayan watanni 6, an sako daliban kwalejin da aka sace a Kebbi

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164