Nasara daga Allah: Sojoji sun yi wa yan bindiga kwantan bauna, sun bude musu wuta a Kaduna
- Jami'an rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar hallaka yan ta'adda biyar a wata musayar wuta a jihar Kaduna
- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, yace sojojin sun samu bayanan sirri kuma suka ɗauki mataki nan take
- Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya yaba wa kwazon sojojin tare da rokon su cigaba da jajircewa a yaƙin da suke
Kaduna - Dakarun sojin Najeriya sun dakile wani hari kuma suka hallaka yan ta'adda biyar a kauyen Kwanan Bataro, karamar hukumar Giwa, jihar Kaduna.
A bayanan da muka samu, sojojin na aikin sintiri a ƙaramar hukumar Giwa yayin da suka samu sahihin bayanin sirri na motsin yan bindiga zuwa garin Fatika.
Wannan dai na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar a shafinsa na Facebook.
Bayan samun bayani, Sojojin suka shirya wa yan ta'addan tarko a Marke da Ruheya.
Yadda fafatawar ta kasance
Wani sashin sanarwan yace:
"Yayin da suka ga sojojin, sai suka yi kokarin guduwa. Amma dakarun sojin suka sha gabansu a Kwanan Bataro kuma suka bude musu wuta."
"Yayin fafatawar ne sojojin suka hallaka yan ta'adda biyar. Bayan kammala tsaftace yankin jami'an sojin sun koma sansanin su."
El-Rufa'i ya yaba da kwazon sojojin
Mista Aruwan, ya ƙara da cewa gwamna Malam El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya nuna jin daɗinsa da gamsuwa da samun wannan bayanin.
Kazalika gwaman ya yaba wa dakarun sojin bisa namijin kokarin da suka yi na ɗaukar matakin gaggawa kan bayanan sirri da suka samu.
Bayan haka, ya kuma roki sojin tare da kara musu gwarin guiwa kan su cigaba da jajircewa a yaƙin da suke da yan ta'adda a yankin.
A wani labarin kuma Sabon bincike ya bankaɗo yadda shugabannin sojoji suka wawure dala biliyan $15bn kudin makamai
Wani sabon rahoto da CDD ta fitar, ya bayyana yadda shugabannin soji da ake naɗawa suka yi sama da makudan kudi cikin shekara 20.
Rahoton ya nuna cewa ta hanyar kwangilar siyo makamai a Najeriya, masu ruwa da tsaki sun yi sama da dala biliyan $15bn.
Asali: Legit.ng