An tura sojoji yaki a Katsina sun koma hada kai da masu hakar ma'adinai, matsala ta bullo

An tura sojoji yaki a Katsina sun koma hada kai da masu hakar ma'adinai, matsala ta bullo

  • Wasu sojojin Najeriya sun yi musayar wuta da masu hakar ma'adinai a wani yankin jihar Katsina ta Arewa maso Yammacin kasar nan
  • Rahotanni sun bayyana cewa, fada tsakanin masu hakon da sojoji ya faro ne kan wani gwal da aka samu a wurin hakar ma'adinai a jihar Katsina
  • Lamarin ya yi muni, inda aka hallaka sojoji biyu kana aka kashe wasu mutum biyu daga cikin masu hakar ma'adinan

Katsina - Sojoji biyu da masu hakar ma'adinai bakwai sun mutu bayan wata arangama da suka yi kan wani tarin gwal da aka gano a garin Magama dake kan iyaka a karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa rikicin ya afku ne a ranar Laraba da misalin karfe 6 na yamma bayan da aka gano gwal din daga cikin wani rami da masu aikin hakar ma’adinan suka tona.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

An hako gwal an kaure da fada
Tashin hankali: Sojoji sun kaure da masu hakar ma'adinai kan wani gwal, an rasa rayuka | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Kimanin mutane 40, masu hakar ma’adinan ba bisa ka’ida ba, wadanda kuma ke dauke da makamai, sun biya sojojin N500,000 kan kowanne rami kafin a barsu su fara aikin hakar ma’adinan.

Ta yaya hakan ta faru?

Daya daga cikin wadanda suka tsira a rikicin ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Lokacin da sojojin suka ga manyan damman da masu hakar ma'adinan suka gano, sai suka dage cewa a raba shi daidai da su.
“Lokacin da masu hakar ma’adinan suka dage cewa ba za su raba dasu ba ko kuma biyan fiye da haka – baya ga Naira miliyan 2.5 da suka biya ramukan guda biyar – sojoji suka fara harbin iska.
“Ma’aikatan hakar ma’adinan da suka firgita, 27 daga cikinsu suna da bindigu, suma sun amsa harbin, sannan aka fara musayar wuta kai tsaye. Sojojin sun rasa jami'ai biyu, yayin da masu hakar ma'adinai suka rasa mutum bakwai a arangamar.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da direban mota tare da fasinjoji 4 a Abuja

“Shugabannin masu hakar ma’adanan sun samu nasarar tserewa da gwala-gwalan da aka kiyasta kimar su a kan Naira miliyan 70 a cikin motarsu.”

Ba a samu jin ta bakin kakakin Rundunar Sojojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Rahoton Daily Trust a a watan Maris din shekarar da ta gabata ya ce shugaba Buhari ya ayyana jihar Zamfara a matsayin yankin hana zirga-zirgar jiragen sama tare da haramta duk wani aikin hakar ma’adinai don dakile ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar.

Biyo bayan dokar hana hakar ma’adanai da gwamnatin tarayya ta yi a Zamfara, majiya ta shaida wa majiyarmu cewa yanzu haka ayyukan sun koma wasu sassan jihar Katsina.

Martanin rundunar sojin Najeriya kan rahoton arangamar sojoji da masu hakar ma'adinai

A bangare guda, rundunar sojin Najeriya ta yi watsi da rahoton na jaridar Daily Nigerian, inda ta ce sam ba gaskiya bane, kana bai da asali daga tushe.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan bindiga sun afka Malumfashi, sun halaka maza 2 sannan sun sace wata mata da yaran ta 2

A cewar sanarwar rundunar ta sojin Najeriya cikin wata sanarwar da Legit.ng ta samo, ta ce:

"Rundunar sojin Najeriya na fatan bayyanawa karara cewa wannan labari ba shi da tushe, kirkirarre ne, ba gaskiya ba ne, kuma kawai tunanin marubuci ne, da nufin bata sunan sojojin Najeriya, domin ba wani sojan Najeriya da aka kashe, kuma ba a yi wata arangama da masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a kauyen Magama ranar 5 ga Janairu, 2022.
"Sabanin kalaman batanci da kafar yada labaran ta yanar gizo ta yada, sojojin Najeriya da aka tura yankin Arewa maso Yamma suna jajircewa wajen yaki da ‘yan bindiga da sauran miyagun laifuka da ke addabar yankin.
"Ba a ba su izinin shiga kowane nau'i na hakar ma'adinai, na halal ko haramtacce ba."

Hakalika, rundunar ta kuma bayyana cewa, ya kamata 'yan Najeriya su nisanta kansu da rahoton da abin da yake kunshe dashi.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Wasu masu tone kabari su sace sassan jikin mamata sun shiga hannu

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda akalla uku a wani samame da suka kai a Damask ta jihar Borno.

Har ila yau, ta ce sojojin sun lalata wata haramtacciyar kasuwa da ‘yan ta’addan ke gudanar da hada-hadarsu, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu, ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.