Yadda wani dattijo ya yaye rufin gidansa don ya biya kudin fansar dansa a Katsina
- Wani dattijo mai suna Saidu Faskari ya yaye rufin gidansa domin ya biya kudin fansar dansa a Katsina
- 'Yan bindiga dai sun fara garkuwa dattijon ne a watan Fabrairu inda ya shafe kwanaki 13 a hannunsu
- A lokacin da dansa ya je biyan kudin fansarsa N50,000 sai maharan suka saki dattijon tare da damke dan nasa
Katsina - Wani manomi a Katsina, Saidu Faskari, ya cire rufin gidansa domin ya siyar yayin da yake tattara kudaden da zai biya fansar babban dansa.
Karamar hukumar Faskari na daya daga cikin yankunan da ke kan gaba a hare-haren da yan bindiga ke kaiwa yankin. Yankin na daya daga cikin wurare 13 da Gwamna Bello Masari ya datse layukan sadarwa daga cikin kokarin magance rashin tsaro.
Wani dan jarida daga Faskari, Ibrahim Bawa ya fada ma jaridar Premium Times cewa dattijon bai samu damar hada kudin fansar ba.
An yi garkuwa da shi kansa Mista Faskari a watan Disamba kuma ya shafe kwanaki 13 a hannun 'yan bindigar.
Lokacin da dansa ya je biyan kudin fansarsa N50,000, sai yan bindigar suka saki dattijon sannan suka tsare dansa.
A yanzu suna neman dattijon ya biya N100,000 a matsayin kudin fansa. Mistan Faskari ya ce yana kokarin ne saboda dansa.
Faskari ya ce:
“Su (’yan fashi) sun yi garkuwa da dana shekaran jiya (Alhamis). Ya je ya biya kudin fansa domin a sake ni. Na shafe kwanaki 13 a sansaninsu. Lokacin da ‘ya’yana suka tara N50,000 sai aka nemi daya daga cikin ‘ya’yana ya kai kudin fansar amma sai ‘yan fashin suka sake ni suka kama shi. Ba ni da abin da zan ci balle a kai ga maganar kudin da zan je in biya fansa.”
Rahoton ya kuma nuna cewa ba a samu damar jin ta bakin kakakin yan sandan jihar, Gambo Isa ba domin wayarsa bata zuwa.
Gwamnatin Zamfara ta daura alhakin sabon harin jihar kan masu yiwa ‘yan bindiga kwarmato
A wani labarin, mun ji cewa yawan mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da yan bindiga suka kai kauyukan jihar Zamfara, a farkon makon nan ya tasar ma 200, The Cable ta rahoto.
A cewar jaridar Punch, wadanda suka tsallake rijiya da baya a harin sun ce 'yan bindiga sun kashe mazauna kauyuka su sama da 200 sannan suka kona gidaje da dama.
Da yake martani a kan harin, Ibrahim Dosara, kwamishinan labaran jihar Zamfara, ya dora alhakin hare-haren akan masu yiwa 'yan bindiga leken asiri.
Asali: Legit.ng