Harajin N10 kan lemun kwalba: Talakawan Najeriya zasu ji jiki, Masana'antun lemu sun gargadi Gwamnati

Harajin N10 kan lemun kwalba: Talakawan Najeriya zasu ji jiki, Masana'antun lemu sun gargadi Gwamnati

  • Kungiyar masana'antun Najeriya tayi tsokaci kan shirin da gwamnati keyi na kakaba kudin haraji kan kayan zaki
  • Masana'antun sun bayyana cewa yan Najeriya zasu ji jiki sabon wannan sabon haraji zai haddasa karin farashin kayan zaki
  • Sun kara da cewa tunanin da gwamnati ke yi na cewa zata samu kudi gurgun tunani ne, fadi zasu yi

Kungiyar masana'antun Najeriya watau MAN ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta sake tunani kan shirin sanya harajin N10 ga litan lemun kwalba da kayan zaki marasa bugarwa.

MAN ta bayyana hakana jawabin da kaddamar inda tace wannan doka na gwamnati asara zai haifar mata ba riba ba, rahoton ThisDay.

A cewar MAN, daga yanzu zuwa 2025, gwamnatin tarayya na iya samun harajin N81bn amma ta rasa N197bn na wasu harajin daban irinsu VAT da CIT daga wajen kamfanonin lemu.

Kara karanta wannan

Don ka yi karatu bai zama dole ka samu aikin Gwamnati ba, Buhari ga Matasan Najeriya

Harajin N10 kan lemun kwalba: Talakawan Najeriya zasu ji jiki, Masana'antun lemu sun gargadi Gwamnati
Harajin N10 kan lemun kwalba: Talakawan Najeriya zasu ji jiki, Masana'antun lemu sun gargadi Gwamnati
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dirakta Janar na MAN, Segun Ajayi-Kadir yace:

"Ina son bayyana cewa kakaba harajin N10/lita kan kayan zaki kan lemun kwalba abin takaici ne."
"Wannan harajin ka iya haifar nuksani wajen biyan albashi, koran ma'aikata da kuma hauhawar farashin kaya."
"Masana'antu zasu so su biya kudin aiki, kuma hakan zai sa su kara kudi da talaka ba zai iya saya ba."

Saboda haka, ya yi kira ga gwamnati ta sake nazari kan wannan shiri, riwayar Punch.

Farashin Coca Cola, Fanta, dss zasu tashi yayinda Gwamnati kara haraji N10 kan litan lemun kwalba

Gwamnatin tarayya ta sanar da karin kudin harajin N10 ga litan dukkan lemukan kwalba marasa bugarwa.

Ministar Kudi, Kasafin Kudi, da shirye-shiryen tarayya, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana cewa an yi wannan kari ne don hana mutane shan kayan kwalba irinsu Coca-Cola, Pepsi, Sprite, dss saboda yawaitan cututukan dake da alaka da Siga irinsu kiba da ciwon siga.

Kara karanta wannan

Farashin Coca Cola, Fanta, dss zai tashi yayinda Gwamnati kara haraji N10 kan litan lemun kwalba

A cewar rahotanni, sama da yan Najeriya milyan hudu ke fama da ciwon Siga sakamakon yawan shan kayan zaki.

Ministar ta bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja yayinda bayani kan kasafin kudin 2022 da Shugaba Buhari ya rattafa hannu, rahoton Leadership.

Asali: Legit.ng

Online view pixel