Neman zaman lafiya: Shugaba Buhari ya jaddada kudurinsa na samar burtali ga Fulani
- Domin samun mafita ga matsalar rashin tsaro da rikicin da ke tsakanin makiyaya da manoma, Buhari ya yi bayani
- Ya sake jaddada manufar gwamnatinsa na wanzar da zaman lafiya ga al'ummar Najeriya baki daya
- Ya ce za a samar da hanyoyin jigilar shanu na Fulani domin kwantar da tarzomar rikici da ake fuskanta
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada kudirin gwamnatinsa na dawo da hanyoyin kiwon shanu a matsayin hanyar magance rikici tsakanin makiyaya da manoma.
Mista Buhari ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan talabijin na Channels da aka watsa a ranar Laraba 5 ga watan Janairu, Premium Times ta rahoto.
Ya ce ya tattauna da ministan noma domin dawo da hanyoyin burtali da aka yi a jamhuriya ta farko musamman a Arewacin Najeriya.
‘Yan Najeriya da dama sun soki wannan manufar, inda suka ce maimakon haka a sanya makiyaya su yi kiwon shanunsu a wuraren kiwo kebabbu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daruruwan mutane ne ake kashewa duk shekara a fadin Najeriya a tashin hankalin da ke tsakanin makiyaya da manoma.
A tattaunawarsa, shugaba Buhari ya yi batutuwa da dama da suka shafi kasar nan, musamman ta fuskar yadda za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Rikicin makiyaya da manoma: Gwamnonin arewa sun soki kiwo a fili
A wani labarin, Gwamnoni a Arewa a ranar Talata sun bayyana batun kiwo a fili da makiyaya suke yi a matsayin tsohon abu. Ya kamata ya kare, The Nation ta ruwaito.
Wannan shawarar ita ce sakamakon taron kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya, wanda aka gudanar.
Shawarar ta yi daidai da ra'ayin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, wanda ya ce ya kamata makiyaya su rungumi kiwo a waje daya su daina kiwon shanun su daga Arewa zuwa Kudu shi ne zaman lafiya.
Majalisar Dattawa ta yi gargadin cewa idan aka bar rikicin manoma da makiyaya ya yi zafi, zai iya haifar da yakin kabilanci da addini da kuma yunwa.
Asali: Legit.ng