Daga Karshe: Gwamnati Buhari amince da ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda

Daga Karshe: Gwamnati Buhari amince da ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta amince da alanta 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda
  • Wannan na zuwa ne yayin da kiraye-kiraye suka yi yawa kan bukatar daukar mataki kan 'yan ta'adda musamman a Arewa
  • A baya dama kotu ta ba da umarnin gwamnati ta amince da wannan bukata, wanda yanzu dai da alamu ya tabbata

Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana aikin ‘yan bindiga a matsayin aikin ta’addanci a hukumance, kamar yadda FIJ ta tattaro.

Abubakar Malami, SAN, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a ne ya bayyana hakan yayin da ya bayyana a shirin ‘Barka da Hantsi’ na gidan Talabijin na Najeriya (NTA) a ranar Talata.

Daga Karshe: Gwamnati ta ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda
Daga Karshe: Gwamnati ta ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Ya ce ofishinsa na aiki don duba hukuncin da kotu ta yanke wanda ya umarci gwamnati ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa babban Malamin addini, Sheikh Saleh Al-Luhaidan, rasuwa

A ranar Laraba, FIJ ta samu takardar, inda Malami ya sanya hannu a cikinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar 26 ga Nuwamba, 2021, Mai shari’a Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya amince da bukatar da gwamnatin tarayya na neman alanta 'yan bindiga da 'yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda.

Bayanan hakan na kunshe ne cikin wata takarda mai taken: ‘Sanarwar Dokar Kare Ta’addanci, 2021’ a juzu’i na 108 na Gazette na Tarayyar Najeriya, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kotun Abuja ta ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda

A tun farko, babbar kotun tarayya ta Abuja ta bayyana kungiyoyin `yan bindiga da ke barna a fadin kasar nan a matsayin 'yan ta'addan.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Mohammad Abubukar, daraktan gurfanarwa (DPP) a ma'aikatar shari'a wanda ya shigar da karar, yace:

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya nada sabbin jami'ai na hukumar gudunarwa ta NNPC

"Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da matakin da ya dauka,wanda babban dalilin hakan shine ganin bayan kungiyoyin `yan bindiga da `yan ta'adda da sauran kungiyoyin ta'addanci a kasar."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.