Jihohin Arewa a gaba-gaba: Inda aka fi amfani da manhajar kudi ta eNaira
- Kudin intanet na Najeriya, eNaira yana samun ci gaba mai yawa kuma ya samu karbuwa a wasu jihohi a kasar
- Jihohin Borno da Gombe da kuma Taraba na daga cikin jahohin arewacin Najeriya da suka karbi manhajar sosai
- Jihar Legas, cibiyar kasuwanci ta Najeriya ba ta cikin manyan jihohi 20 da suka amince da hada-hada da eNaira
Daya daga cikin manyan biranen kasuwancin Najeriya, jihar Legas ya bace cikin manyan jihohin da suka fi karbar tsarin kudin intanet na Najeriya, eNaira.
Bayanai daga Google Trends sun nuna cewa eNaira ta shahara sosai a jihohin Arewacin Najeriya.
Bayanai ba sa karya
Alkaluman kididdigar Nairametric da Legit.ng ta samu sun nuna cewa jihar Borno ce ke kan gaba da 81% cikin 100% na karbar manhajar sai jihohin Sokoto, Gombe da Taraba.
Zamu rikirkita Najeriya idan aka kara farashin fetur da lantarki, Kungiyar kwadago a sakon sabon shekara
eNaira tun daga tushe an yi ta ne da nufin haifar da hada-hadar kudi a yankunan karkara, da kuma jawo jama'ar da ba su da banki zuwa amfani da kudi a saukake.
Ya batun sabon ci gaba daga eNaira?
Masana sun yi hasashen cewa kudin Intanet na Najeriya zai sami karbuwa sosai a shekarar 2022.
eNaira daidai yake da naira ta zahiri kuma ana adana kudi ne a cikinsa a matsayin lalitar yanar gizo.
Rijistar asusun eNaira Speed mai sauki ne kuma yana da ingantattun fasalullukan tsaro wadanda ke tabbatar da kariya ha bayanan masu asusun.
Bankunan da suka fi yawan adadin lalitar masu amfani sun hada da Access Bank, Zenith Bank, First Bank, UBA, Bankin Polaris da Ecobank.
Lalitar 'yan kasuwa dubu 20 ne ke aiki tare da kusan 20% cikin 100% daga bankunan Ecobank, Union Bank, Stanbic IBTC, da Ecobank.
A wani labarin, manhajar eNaira ta yi batan dabo daga kan Google Play Store kimanin kwanaki biyu bayan kaddamar da ita, rahoton Punch ya nuna haka.
Wannan ya faru ne bayan sama da mutum 100,000 masu amfani da waya kalar Android sun saukar da manhajar don amfani.
Amma ga masu wayar iPhone, manhajar har yanzu tana nan kuma ana cigaba da amfani da ita.
Asali: Legit.ng