Ka tuna da alkawarin da ka dauka: 'Yan Arewa sun roki Buhari kada ya basu kunya a 2022
- Ana kara matsa lamba ga shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa ya kare al'ummar Arewacin Najeriya daga kashe-kashe
- Wata fitacciyar kungiyar Arewa mai suna Arewa Consultative Forum ta ce ya zama wajibi shugaban kasa ya kare dukkan ‘yan Najeriya
- A wani sabon sako da ta fitar, kungiyar ta kalubalanci shugaban kasar da ya cika alkawarin kare al'umma dukiyoyinsu
Kaduna - Arewa Consultative Forum (ACF) ta roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gyara matsalar tsaro a kasar nan a shekarar 2022, inda ta tunatar da shi cewa wannan shi ne dalilin da ya sa akasarin ‘yan Najeriya suka zabe shi a zaben 2015.
Kungiyar ta shaida wa shugaban kasar da jami’an tsaronsa cewa ‘yan Najeriya na son samun kwanciyar hankali da aminci a ko’ina a kasarsu daga wannan shekara.
Kakakin ACF, Emmanuel Yawe, wanda ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Nigerian Tribune a ranar Asabar 1 ga watan Janairu, ya kuma bukaci gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi da su marawa gwamnatin tarayya baya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce dole ne kowa ya tashi tsaye wajen yin amfani da hanyoyin da za a bi wajen tunkarar matsalar ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka a arewacin Najeriya.
Yace:
“Ya dace shugaban kasa ya kare al’ummar kasar daga hannun ‘yan Boko Haram, masu garkuwa da mutane, barayin shanu, ‘yan fashi da makami, da dai sauransu.
“Muna so mu ga cewa an kama wadanda ke da hannu a wadannan munanan ayyukan kuma an gurfanar da su a gaban kuliya. Ta haka ne kawai yanayin tsaro zai canza. Idan har aka bar masu wannan aika-aika su ci karensu ba babbaka ba tare da wata matsala ba, yaushe rashin tsaro a kasarmu zai kau?
“Dole ne kowa ya hada hannu don ganin an shawo kan kalubalen tsaro a 2022. An kashe manoma da yawa. Yawancin manoma sun yi watsi da gonakinsu. Karancin abinci ya kunno kai. Ana yi wa tarbiyyar yaranmu barazana. Asibitocin mu sun zama babu kowa a ciki. Dole ne gwamnati ta kowace hanya ta dauki mataki."
Adadin 'yan ta'adda da aka kashe a 2021
A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta yi duba ga yakin da take yi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan a shekarar 2021, inda ta ce ta samu nasarar dakile ‘yan tada kayar baya da dama.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda ya yi jawabi ga taron manema labarai a Legas, ya ce an kashe ‘yan ta’adda a kalla 1000, Daily Trust ta rahoto.
Ya ce yayin da mahara 22,000 suka mika wuya, an ceto fararen hula 2000 tare da kwace dimbin makamai da alburusai, ya kara da cewa an lalata wasu masana’antun sarrafa bama-bamai na ISWAP da ‘yan ta’addan Boko Haram.
Mohammad ya amince da cewa babban kalubalen da gwamnatin tarayya ta fuskanta a shekarar 2021 shi ne matsalar tsaro, kamar yadda Punch ta rahoto.
A wani labarin, rahoton Daily Trust ya bayyana yadda Gamayyar Kungiyoyin Arewa ta CNG ta koka kan yadda kashe-kashe, garkuwa da mutane, da rashin tsaro ya addabi yankuna a fadin kasar nan.
Daraktan Sadarwa na kungiyar ta CNG, Ismail Musa ya ce kamata ya yi shugaba Buhari ya mai da Najeriya yadda ya same ta a hannun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Musa, wanda ya yi wannan kiran a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a ranar Laraba kai tsaye ta jaridar Vanguard, ya caccaki shugaban kasar Najeriya na yanzu kan yadda yake tafiyar da harkokin tsaro a kasar.
Asali: Legit.ng