Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wasu kasuwanni biyu a jihar Sokoto, ta kone shaguna
- Wata mummunar gobara ta tashi a jihar Sokoto, inda ta kone wasu shaguna sama da 150 cikin kankanin lokaci
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, kasuwanni biyu da suka kama da gobarar sun tafka asarar miliyoyi a jiya Laraba
- Hakazalia, kwamishinan kasuwanci da masana'antu na jihar ya kawo ziyara wurin domin gane wa idonsa abin da ya faru
Sokoto - Gobara ta kone kasuwanni biyu; Kasuwan Daji da Kasuwar Kara da ke Sokoto a ranar Larabar da ta gabata tare da lalata kayayyakin da darajarsu ta kai na miliyoyin Naira.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa gobarar da ta tashi da misalin karfe 11:30 na safe har zuwa yamma inda ta lalata sama da shaguna 150 a Kasuwan Daji.
Gobarar da ta tashi a kasuwar Kara kuma da misalin karfe 7 na dare ta yi barna har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Jami’an kashe gobara na tarayya da na jihar Sokoto suna ta fafatawa don ganin sun shawo kan kashe ta.
Kawo yanzu dai ba a iya gano musabbabin tashin dukkanin gobara guda biyun ba.
Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar, Bashir Jegawa, wanda ya ziyarci Kasuwan Daji, ya ce za a kafa kwamitin da zai tabbatar da barnar da aka yi domin samar da tallafi.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta jihar Sokoto, Alhaji Chika Sarkin Gishiri, ya ce ‘yan kasuwa sun yi asarar kayayyakin da suka kai na miliyoyin naira.
Ana yawan samun gobara a Najeriya, lamarin da yake jawo asarar kayayyaki da dukiyoyi a Najeriya.
A makon jiya, wata gobara ta tashi a jihar Kano, inda ta kone wani katafaren kamfanin sayar da kayayyakin gidaje, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rahoto.
Matasa sun shiga hannu yayin da suke kokarin satan kaya a wurin gobara a Abuja
A wani labarin daban, rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta kama wasu mutane uku da suka yi yunkurin wawure wasu kayayyaki daga babban kanti na Next Cash and Carry da gobara ta kame a safiyar Lahadi.
Daily Trust ta ruwaito cewa, a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a yanar gizo, an ga matasa suna tura keken daukar kaya da ake zargin sun yi amfani da su wajen fitar da abubuwan suka sace.
Sai dai da take karin haske kan halin da ake ciki a cikin wata sanarwa, rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta bakin mai magana da yawunta, Josephine Adeh, ta ce ba a sace kaya a kantin ba.
Adeh, ta bayyana cewa jami’an 'yan sanda da sauran jami’an tsaro sun kai dauki cikin gaggawa domin ganin an kashe gobarar da kuma hana sace-sace a kantin.
Asali: Legit.ng