Al’umman Zamfara sun yi bikin cika wata daya ba tare da hari ba, in ji Audu Bulama Bukarti
- Rahotanni sun kawo cewa al’umman wani gari a jihar Zamfara sun yi bikin cika wata daya ba tare da hari daga yan bindiga da ke zirya a yankunansu ba
- Sai dai hakan bai kasance sakamakon kokarin gwamnati ba kamar yadda Audu Bulama Burkati, wani mai rajjin kare hakkin dan Adam ya bayyana
- Audu Bulama Burkati ya yi ikirarin cewa maimakon mutanen sun yarda da gwamnati, sun kulla yarjejeniya da yan bindigan
Zamfara - Mazauna garin Dansadau da ke jihar Zamfara sun yi bikin wata daya ba tare da harin yan bindiga ba. Audu Bulama Bukarti, wani mai rajjin kare dan Adam ne ya bayyana hakan.
A cewarsa, wannan bikin bai kasance sakamakon kokarin gwamnati ba. Ya ce yan bindigar basu kai wa mutanen hari ba saboda sun kulla yarjejeniya da su.
Ya ce:
“A yau, mutanen Dansadau na Zamfara sun yi bikin cika wata daya ba tare da hari ba. Amma kafin Ku fara jinjinawa da zagin manyan masu fada aji...Wannan bai kasance sakamakon kokarin gwamnati ba. Ya kasance ne saboda mutanen Dansadau sun kulla yarjejeniya da yan ta’addan. Sun ce sun mika wuya ga yan ta’addan saboda gwamnati ta gaza masu. Shin akwai gazawar da ta fi ta gwamnati? Menene aikin gwamnati?”
A halin da ake ciki, jama’a sun gaggauta yin martani ga wallafarsa, inda mutane da dama suka goyi bayan matsayinsa yayin da wasu suka yi adawa.
Auwalu Minkaila
“Abun da ke faruwa a Najeriya ya saba gaba daya. Babban aikin gwamnati shine kare rayuka da dukiyoyin al’umma, alamu sun nuna cewa akwai gwamnatoci biyu da ke aiki a Najeriya, zancen gaskiya, ba mu da gwamnati mai kula. Shugabanninmu suna nan suna tara dukiya, suna jefa al’ummansu a talauci da mawuyacin hali.”
Abubakar Muhammad Dekau
“Amma barista shin kana ganin daura laifuka mara ma’ana kan gwamnati kadai zai magance abubuwa a kasar nan? Ni Ina ganin cewa kamata yayi jama’ar kasar baki daya mu sauya halayenmu ba tare da la’akari da banbancinmu ba domin Allah ya kubutar da mu. Amma bana ganin yada wannan sukar zai haifar da ‘ya’ya masu idanu.”
Bashir Kabir Kutawa
“Yan siyasar Najeriya sun wofantar da hakkin gwamnati. Muna zaman dar-dar da bakin ciki.”
Mohd N Ismail
“Mutanen Dansadau sun yi kokari, amma gwamnati ta gaza ta kowani bangare, musamman a bangaren tsaro, kuma a kullun suna batawa mutane rai da cewar suna iya bakin kokarinsu.”
Musa Abdullahi
“Shakka babu babban hakkin da ya rataya a wuyan kowace gwamnati mai kishi shine kare rayuka da dukiyoyin talakawanta. An ji kunya!”
'Yan sanda sun ragargaji mafakar tsageru a Jigawa, an kame mutum 7
A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mutum bakwai a yayin wata mamaya da ta kai mafakar yan ta'adda a kananan hukumomin Birnin kudu da Gwaram da ke jihar.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da kamun ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a Dutse ranar Talata.
Shiisu ya ce an kama uku daga cikin wadanda ake zargin masu shekaru tsakanin 20 da 28 a kauyen Babaldu, karamar hukumar Birninkudu lokacin da tawagar 'yan sanda suka kai mamaya mafakar tsageru da ke yankin.
Asali: Legit.ng