Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun hallaka Basarake da wasu mutane a jihar Zamfara

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun hallaka Basarake da wasu mutane a jihar Zamfara

  • Wasu miyagun yan bindiga sun kashe basarake a wani sabon hari da suka kai yankin masarautar Bungudu, jihar Zamfara
  • Mazauna kauyen Gada sun bayyana cewa maharan sun cinna wuta a motocin masarauta da kuma kayan abincin da suka taras
  • Masarautar Bungudu ta sanar da cewa za'a gudanar da jana'izar basaraken da mutum uku da maharan suka kashe da karfe 4:00 na yamma

Zamfara - A ranar Laraba, wasun tsagerun yan bindiga sun kai hari kauyen Gada, dake ƙaramar hukumar Bungudu a jihar Zamfara, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun kashe basaraken kauyen, Umaru Bawan-Allah, da wasu mazauna uku yayin harin.

Sakataren masarautar Bungudu, Usman Ahmad, ya bayyana cewa maharan sun farmaki kauyen da misalin karfe 1:00 na dare, inda suka aikata wannan aika-aika.

Kara karanta wannan

Hatsarin jirgin ruwa ya halaka magidanci, matansa biyu da dansa a Neja

Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun hallaka Basarake da wasu mutane a jihar Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kauyen Gada na da nisan kilomita bakwai daga garin Bungudu, hedkwatar ƙaramar hukumar Bungudu a jihar Zamfara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An sanar da lokacin jana'iza

Mista Ahmad ya kara da cewa majalisar masarauta ta sanar da karfe 4:00 na yammacin yau Laraba a matsayin lokacin da za'a gudanar da jana'izar basaraken da sauran mutanen da aka kashe.

Wannan na zuwa ne watanni uku bayan sace sarkin masarautar Bungudu, Hassan Attahiru, a kan babbar hanyar Kaduna-Abuja a watan Satumba.

Amma yan bindigan sun sako shi bayan kwanaki 32, kuma ana ganin shi ne ke sama da basaraken Gada, wanda aka kashe yau Laraba.

Yadda lamarin ya faru

Mazauna a yankin sun bayyana cewa maharan sun kwashi kimanin awanni hudu suna kashe mutane, jikkata wasu da kuma cin zarafin mata.

Haka nan sun ce yan bindigan sun cinnawa motoci da kayan abinci da aka ajiye a harabar gidan basaraken, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ragargaji mafakar tsageru a Jigawa, an kame mutum 7

Lambar wayan kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, Muhammad Shehu, ta ki shiga ya yin da akayi kokarin jin ta bakin hukumarsu.

A wani labarin na daban kuma Kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya aike da wasikar neman sulhu ga shugaba Buhari, Matawalle

Sanannen ɗan bindigan nan da ya addabi yankunan jihar Zamfara, Bello Turji. ya nemi a sulhu da gwamati da sarakunan gargajiya.

Wannan na zuwa ne bayan dakarun sojin sama da ƙasa sun ƙara ƙaimi kan yan bindiga bayan kotu ta ayyana su yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262