Amaechi makaryaci ne, Jonathan ya bar $28.6bn a asusun kasar waje na Najeriya, Omokri

Amaechi makaryaci ne, Jonathan ya bar $28.6bn a asusun kasar waje na Najeriya, Omokri

  • Hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya musanta batun cewa kudaden da tsohon shugaban kasar ya bari a asusu a 2015 basu wuci makwanni uku ba su ka kare
  • Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa kudaden da Jonathan ya bari ba su wuci makwanni 3 ba, furucin da ya tunzura Omokri har ya ja ya karyata shi
  • A cewar Omokri, a ranar 29 ga watan Mayun 2015, Jonathan ya bar dala biliyan 28.6 a ajiyar kudaden kasar waje, dala biliyan 2.2 a asusun man fetur da dala biliyan 5.6 na kudin sinadarin gas

Reno Omokri, hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya musanta batun cewa kudaden da tsohon shugaban ya bari sun kare bayan kimanin makwanni uku a 2015, Arise Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Minista ya tona asiri, ya ce Jonathan bai bar wa Buhari komai a asusun Najeriya ba

Dama ministan sufuri, Rotimi Amaechi ne ya yi wannan ikirarin.

Amaechi makaryaci ne, Jonathan ya bar $28.6bn a asusun kasar waje na Najeriya, Omokri
Reno Omokri ya karyata Ameachi kan ikirarin cewa Jonathan bai bar isasun kudi a asusun Najeriya ba. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Omokri ya musanta wannan batun ta shafinsa na Instagram inda ya ce Amaechi ya dade yana nuna burinsa na tsayawa takara a matsayin mataimakin shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC.

Ya ce hakan yasa ya ke nemo karairayin da zai yi akan mulkin Goodluck Jonathan.

Omokri ya kira Amaechi da makaryaci

Reno Omokri, wanda hadimin Jonathan ne na harkar labarai ya kwatanta Amaechi a matsayin “makaryaci.”

Kamar yadda ya wallafa:

Ga asalin abinda Jonathan ya bari a ranar 28 ga watan Mayun 2015, da Amaechi ya ce ba su ishi Najeriya yin makwanni uku ba:

"Ajiyar kudade na kasar waje ta dala biliyan 28.6, dala biliyan 2.2 a asusun rarar kudin man fetur sai kuma rarar sinadarin gas ta dala biliyan 5.6 har da dala bilyan daya na hannun jari ta Nigeria Sovereign Investment Authority.”

Kara karanta wannan

Sanata Shehu Sani ya gwangwanje jami'an kan hanya da kyautukan kirsimeti a Kaduna

Yayin da ya ke martani akan zargin da ake yi wa Jonathan na barin kudaden da basu wuci amfanin makwanni uku ba ga kasa, Omokri ya zargi Amaechi da zama dan gani kashe nin shugabannin sa.

Ya yanko daidai wurin da Amaechi a wata tattaunawa da Channels TV ta yi da shi yace kudin da Jonathan ya sauka daga mulki ya bari a 2015 ba su ishi Najeriya yin makwanni uku ba.

Kamar yadda ya wallafa:

“Rotimi Amaechi makaryacin banza ne, a tunaninsa zai samu matsayin mataimakin shugaban kasa ne a karkashin APC idan ya caccaki shugaban kasa Jonathan. 2023 ta kusa. Gabadaya ‘yan Najeriya za su ga abinda Buhari zai bari idan ya sauka banda bashin naira tiriliyan 40.”

Ya ce dama can Amaechi kaskantacce ne

A cewarsa Amaechi ya fara rayuwa ne a matsayin hadimin Peter Odili, don haka har yanzu kaskanci bai bar shi ba.

“Har yanzu yana da matsalar daukan kansa da daraja kuma dama an ja kunnen ‘yan Najeriya akan gazgata maganarsa,” a cewar Omokri.

Kara karanta wannan

Bishop Kukah: Allah bai yi kuskure ba da ya hallici mutane masu addinai da ƙabilu daban-daban a Najeriya

Ya bayyana batun yadda yanzu haka Amaechi ido rufe yake neman tikitin tsayawa takarar mataimakin shugaban kasa a APC akan tunanin dan arewa jam’iyyar za ta tsayar a matsayin shugaban kasa.

Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa

A waGwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta JIhar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.

A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'

Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.

Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa

Kara karanta wannan

Takarar 2023 na neman raba kan Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo da Ubangidansa Tinubu

A wani labarin, Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta JIhar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.

A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'

Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164