'Ƴan ISWAP suna tattara kansu domin su kawo mana hare-hare' - Mazauna Borno sun koka

'Ƴan ISWAP suna tattara kansu domin su kawo mana hare-hare' - Mazauna Borno sun koka

  • Mazauna Chibok da Damboa da ke jihar Borno sun bayyana damuwarsu akan yuwuwar mayakan ISWAP su kai musu farmaki a ko wanne lokaci
  • A ranar Talata da safe wasu mazauna yankunan su ka bayyana wa manema labarai hakan inda su ka ce sun lura da yadda ‘yan ta’addan su ke taruwa a Gumsuri Litawa tun ana gobe kirsimeti
  • A cewarsa, su kan taru ne a wani wuri idan su na shirin kai farmaki yankin, don tsakanin inda su ke taruwa da Chibok da Damboa bai wuci tafiyar kilomita 12 zuwa 22 ba

Jihar Borno - Mazauna garuruwan Chibok da Damboa sun koka akan yiwuwar mayakan ISWAP su kai musu hare-hare a ko wanne lokaci, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 7 tare da garkuwa da wasu da dama a wasu kauyuka

'Ƴan ISWAP suna tattara kansu domin su kawo mana hare-hare' - Mazauna Borno sun koka
Mutanen Borno sun ce 'yan ta'adda na shirin kai musu hari. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Wasu mazauna yankunan sun kira wakilin The Cable da safiyar Talata inda suka bayyana damuwarsu akan yadda mayakan suke yawan taruwa a Gumsuri Litawa tun ana gobe Kirsimeti.

Gumsuri Litawa wani gari ne da bai wuce kilomita 12 zuwa 22 ba zuwa Chibok da Damboa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mazaunan sun ce al’adar mayakan ne irin wannan taron idan su na shirin kai farmaki

Su kan yi irin wannan taron ne kamar yadda mazauna yankin su ka shaida idan su na da shirin kai hari garin.

Kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida:

“Idan su na irin wannan taron, za ka ga babu dadewa su ke kai wa garuruwa farmaki.”

The Cable ta gano yadda yanzu haka mazauna yankin su ka sanar da sojoji don su yi gaggawar kai wa yankunan dauki, sai dai har yanzu babu wani matakin da aka dauka.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kai Wa Matafiya Hari, Sun Sace Da Dama a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari

Akwai hedkwatar sojin kasa a Damboa

Duk da hedkwatar sojin kasa ta brigade 25 ta ke a Damboa sannan taskforce brigade 27 a Chibok take.

Daya daga cikin mazauna yankin ya shaida wa The Cable cewa:

“Rundunar soji ta kan yi sintiri a wuraren amma yanzu ban san dalili ba, ta daina.”

Ba a samu damar tattaunawa da kakakin rundunar sojin, Onyema Nwachukwu ba, don jin ta bakinsa akan wannan lamarin.

Dama sun taba kai farmaki yankin

A watan Oktoba, mayakan sun kai farmaki Damboa da motocin yaki guda 15.

Sun halaka kwamandan rundunar soji da ke Chibok, Dzarma Zirkusu a watan Nuwamba.

Ana saura kwana biyu bikin kirsimeti, mayakan ISWAP su ka harba makamai masu linzami a Maiduguri, babban birnin jihar, yayin da shugaba kasa Muhammad Buhari zai kai ziyara jihar.

Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna

A baya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.

Kara karanta wannan

Mutanen Kaduna sun maida martani ga kalaman gwamna El-Rufa'i na aika yan ta'adda lahira

A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.

Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164