Zamfara: Hayar bindiga muke yi domin sheke mutane da satar shanu, 'Yan bindiga 3

Zamfara: Hayar bindiga muke yi domin sheke mutane da satar shanu, 'Yan bindiga 3

  • Hukumar NSCDC ta sanar da kama wasu mutum 3 da ake zargin 'yan bindiga ne a tashar mota da ke Gusau yayin da suke kokarin barin garin
  • 'Yan bindigan sun amsa yadda suke kashe mutane tare da satar Shanu a kauyukan Zamfara ta hanyar amfani da bindigun haya
  • Ikor Oche, kakakin hukumar, ya ce mutum 3 da ake zargin sun nuna masa cewa jihar Taraba suka nufa domin tarar da 'yan uwansu da ke can

Gusau, Zamfara - Hukumar NSCDC ta tabbatar da damke wasu mutum uku da ake zargin 'yan bindiga ne yayin da suka tsere zuwa yankin Magami da ke Zamfara sakamakon ruwan wuta da sojoji ke musu.

Ikor Oche, kakakin hukumar NSCDC, ya tabbatar da wannan cigaban a taron manema labarai inda yace wadanda aka kaman sun shiga hannu ne yayin da suke tashar mota da ke Gusau a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke mutum 7 a kusa da matsayar sojoji, sun sace wasu a Katsina da Kaduna

Zamfara: Hayar bindiga muke yi domin sheke mutane da satar shanu, 'Yan bindiga 3
Zamfara: Hayar bindiga muke yi domin sheke mutane da satar shanu, 'Yan bindiga 3. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Oche ya ce an kama wadanda ake zargin da safe yayin da suke kokarin shiga mota zuwa Taraba domin haduwa da sauran miyagun da suka koma can, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce: "Tukur Halilu mai shekaru 27 dan asalin kauyen Gabaru ne da ke yankin Nahuche a karamar hukumar Bungudu ta jihar karkashin gagarumin shugaban 'yan bindiga, Magajin Kaura".

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta ruwaito cewa, kamar yadda yace, Halilu ya tabbatar da cewa ya na satar shanu a dukkan kauyukan da ke karamar hukumar.

Ya ce sauran biyun da ake zargin su ne Hussaini Altine mai shekaru arba'in da Abubakar Altine mai shekaru sittin duk daga kauyen Agamalafiya, gundumar Rijiya da ke karamar hukumar Gusau.

"Duk da Abubakar Altine ya ce babu ruwan shi, Hussaini ya tabbatar da cewa ya na daga cikin 'yan kungiyar gagararren dan bindiga Gugurawa," yace.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mata masu juna biyu sun haihu a kan tsaunuka garin gujewa'yan bindiga

Kakakin hukumar NSCDC, ya ce Hussaini Altine ya na daga cikin miyagun da suka kai farmaki uku na Kurya,, Bagawuri, Agamalafiya da Rijiya.

Ya kara da cewa, wadanda ake zargin ana tuhumar su wanda hakan zai iya sa a sake damko wasu kafin a gurfanar da su.

Zamfara: Sanata Marafa ya magantu kan zarginsa da ake da alaka da 'dan bindiga

A wani labari na daban, daya daga cikin shugabannin jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Sanata Kabiru Garba Marafa, ya ce ba ya da alaka da gawurtaccen dan bindigan nan, Abdulmuminu Moossa a jihar Sokoto.

Sanatan ya bukaci ‘yan sanda, jami’an hukumar DSS da sauran jami’an tsaro da su gabatar da rahoton da zai nuna alakarsa da Moossa, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a wata takarda wacce ofishin kamfen din sanatan ya saki a ranar Juma’a, ya ce lokaci ya yi da ya kamata jami’an tsaro su jajirce wurin yin bincike akan matsalar tsaron kasar nan.

Kara karanta wannan

Jama’a Sun Shiga Tashin Hankali Bayan Ƴan Bindiga Sun Fatattaki Manoma Daga Gonakinsu, Sun Kuma Sace 2 a Abuja

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng