Ministan Buhari ya gana da kamfanin Jamus kan yadda za a bullowa aikin jirgin Maradi-Kano

Ministan Buhari ya gana da kamfanin Jamus kan yadda za a bullowa aikin jirgin Maradi-Kano

  • Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi ya yi zama da masu aikin titin jirgin kasan Kano-Maradi
  • Rotimi Amaechi ya hadu da wakilan bankin KfW-IPEX a kan yadda za a shawo kan aikin da wuri
  • Jakadan Najeriya a kasar Jamus, Yusuf Tuggar ya na cikin wadanda suka halarci taron a Berlin

Berlin - A ranar Alhamis, 23 ga watan Disamba, 2021, Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya gana da kamfanin da ke bada shawara kan aikin dogon Kano-Maradi.

Jaridar Vanguard tace an yi wannan zama ne domin a hanzarta aikin gina titin jirgin kasa daga garin Kano zuwa Jamhriyyar Nijar nan da makonni masu zuwa.

An yi wannan muhimmin zama ne ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Berlin a kasar Jamus, tare da wakilai daga babban bankin KfW-IPEX na kasar Jamus.

Kara karanta wannan

Coca Cola ta kaddamar da 'Project EQUIP' a Kano: Ga Muhimman abubuwa 3 da shirin zai mayar da hankali a kai

Bankin KfW-IPEX ne suke aiki a matsayin masu ba kamfanin African Finance Corporation da aka ba kwangilar titin jirgin kasan shawara da bashin kudin yin aiki.

Rotimi Amaechi yace kamfanonin ketare za su iya zuwa Najeriya domin sa ido, su tabbatar da cewa an bi ka’idoji wajen wannan kwangila da ake shirin farawa.

Buhari
Buhari a jirgin kasa Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Sundiata Post tace Ministan ya tabbatarwa kamfanin cewa ba za a samu matsala wajen aikin ba, domin ba za a bari titin jirgin ya ratsa ta tsakanin garuruwa ba.

Gwamnatin Najeriya za ta iya biyan bashin?

Wani jami’in bankin KfW-IPEX, Dr. Carsten Wiebers ya bayyana cewa su na sa rai gwamnatin Najeriya za ta iya yin wannan aiki, ta biya duk bashin da ta karba.

Ganin cewa a cikin watanni 15 ake so ayi aikin, Dr. Carsten Wiebers ya bada shawarar a tanadi duk wasu takardu da ake bukata domin wannan aiki ya kankama.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona

Darektan sufuri na bankin KfW-IPEX, Sylvia Sedlacek ya yi alkawari cewa za su fitar da rahoto da zai nuna tasirin da wannan aiki zai yi wa Najeriya da kasar Nijar.

Sedlacek yace za su hada-kai ne da ma’aikatun sufuri, muhalli, da gidaje domin ayi wannan bincike.

Daga cikin wadanda suka yi jawabi a wajen zaman akwai Jakadan Najeriya zuwa Jamus, Yusuf Tuggar wanda yace gwamnatin Najeriya ta shirya bin duk wata doka.

Mulkin Najeriya sai Osinbajo

A ranar Alhamis, 23 ga watan Disamba, 2021, aka ji tsohon shugaba Janar Ibrahim Babangida ya yi magana kan batun 2023, yace YemiOsinbajo ya cancanta da mulki.

Ibrahim Badamasi Babangida ya fadawa magoya bayan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo cewa su fada masa ya jajirce a kan neman mulki a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel