Osinbajo ya fi dacewa da rikon Najeriya - Tsohon Shugaba Babangida ya fadi abin da ya hango

Osinbajo ya fi dacewa da rikon Najeriya - Tsohon Shugaba Babangida ya fadi abin da ya hango

  • Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yabi Yemi Osinbajo, yace zai iya rike Gwamnatin Najeriya
  • Ojo Foluso ya jagoranci ‘yan kungiyarsu ta Osibanjo Grassroots Organisation zuwa wajen Janar IBB
  • Ibrahim Babangida ya yi kira ga Farfesa Osinbajo ya dage, ya nemi takarar shugabancin kasar nan

Minna - Yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara, Ibrahim Badamasi Babangida wanda ya yi shugaban kasa a lokacin mulki soja, ya tabo batun siyasar 2023.

A ranar Alhamis, 23 ga watan Disamba, 2021, jaridar Daily Trust tace Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya nuna goyon baya ga Yemi Osinbajo a zaben 2023.

Ibrahim Babangida ya bayyana wannan ne da ya gana da wasu magoya bayan mataimakin shugaban kasar a inuwar tafiyar Osibanjo Grassroots Organisation.

‘Yan kungiyar a karkashin jagorancin Ojo Foluso sun ziyarci Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya a gidansa da ke garin Minna, jihar Neja a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Wanda ya yi wa Buhari Minista a 1984 ya kawo shawarwarin yadda za a magance rashin tsaro

Rahoton yace Janar Babangida ya yi kira ga Farfesa Yemi Osinbajo ya tsaya tsayin-daka, ya nemi takarar shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa na shekarar 2023.

Osinbajo
Buhari da Osinbajo Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me Janar Babangida ya fada game da Osinbajo?

“Na san mataimakin shugaban kasar da kyau. Mutumin kirki ne. Mutumin da ya yi imani da Najeriya, wanda jama’a za su iya sauraronsa, ya zaburar da su.”
“Ya dace ayi aiki da mutum irin wannan. Mu na bukatar mutumin kwarai ya rike Najeriya.” – IBB.

A cewar Janar IBB, Osinbajo mutumi ne da yake da kishin kasa, yace dole ne duk wanda za a bar wa shugabanci, ya fahimci halin al’umma kafin ya iya jagorantar su.

“Ina so in aika sakon Allah ya bada sa’a ga Osinbajo ta bakinku. Ina so in fada masa cewa ya jajirce. Na san da wahala, amma zai iya. Allah ya ba shi sa’a.” – IBB.

Kara karanta wannan

Babban Basarake ya mutu a Kaduna, Buhari da Gwamna El-Rufai sun aiko sakon ta’aziyya

Kamar yadda This Day ta rahoto, Babangida yace ya yarda ya zauna da kungiyar ne domin ya san Osinbajo ya na da abin da ake bukata wajen zama shugaba na gari.

Buhari ya na ban-kwana?

Dazu aka ji cewa Mai girma Shugaba Muhammadu Buhari ya fara sallama da ‘Yan Najeriya, ya yi magana a game da abin da yake so wanda zai gaje shi ya yi a mulki.

Da yake jawabi a garin Maiduguri, Buhari ya tuna da abin da ya faru da shi a 1985, yace an daure shi bayan ya sauka daga kan mulkin soja, daga baya aka fito da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel