Buhari ga hafsoshin tsaro: Ku murkushe Boko Haram kafin 2023

Buhari ga hafsoshin tsaro: Ku murkushe Boko Haram kafin 2023

  • A ranar Juma'a, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci hafsoshin tsaro da su murkushe Boko Haram kafin zuwan 2023
  • Shugaba Buhari ya sanar da hakan ne yayin da ya yi taro da majalisar tsaro a Abuja bayan dawowarsa daga Maiduguri, Borno
  • Buhari ya ce kada a bar ko inci daya na kasar nan a hannun 'yan ta'adda, kuma a shirya nasara kan yaki da 'yan ta'adda nan babu dadewa

FCT, Abuja - A jiya Juma'a, hafsoshin tsaro sun samu sabon umarni daga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan cewa su mitsike 'yan ta'addan ISWAP, wadanda suka maye gurbin Boko Haram a ta'addancin arewa maso gabas, kafin shekarar da wa'adin mulkinsa zai cika.

The Nation ta ruwaito cewa, Buhari ya bayar da wannan umarnin a taron majalisar tsaro da suka yi a Abuja, sa'a ashirin da hudu bayan da 'yan ta'addan suka yi ruwan makamai masu linzami a filin jirgin sama na Maiduguri kafin isar shugaban kasa garin.

Kara karanta wannan

Bayan farmakin ISWAP a Borno, Buhari yace ana matakin karshe na yaki da 'yan ta'adda

Mutane masu tarin yawa sun rasa rayukansu sakamakon harba makaman masu linzami.

Buhari ga hafsoshin tsaro: Ku murkushe Boko Haram kafin 2023
Buhari ga hafsoshin tsaro: Ku murkushe Boko Haram kafin 2023. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Alkali Baba Usman, ya ce tuni an cilla wasu daga cikin wadanda suka yi farmakin lahira.

The Nation ta tattaro cewa, a yayin taron majalisar tsaron, Buhari ya bada umarnin cewa, kada a bar ko inci daya na kasar nan a hannun 'yan ta'adda.

Buhari ya yi mamakin dalilin da yasa 'yan ta'addan ISWAP suke cigaba da kai farmaki daga wuri daya ba tare da an dakile su ba, kuma ya yi kira ga shugabannin tsaron da su shirya samun nasara kan yaki da ta'addanci kafin ya bar kujerarsa.

Wa'adin mulkin shugaban kasan na biyu zai kare a watan Mayun 2023.

Buhari ya ce da gaske ya ke akan abinda ya sanar da dakarun sojin a Maiduguri kan bukatar a kakkabe 'yan ta'addan Boko Haram da na ISWAP.

Kara karanta wannan

Babu sauran sassauci tsakanin mu da yan bindiga, musamman a arewa, Shugaba Buhari

Bayan farmakin ISWAP a Borno, Buhari yace ana matakin karshe na yaki da 'yan ta'adda

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga dakarun sojin rundunar Operation Hadin Kai da su cigaba da kokari yayin da suke shiga matakin karshe na yaki da ta'addanci.

Kamar yadda sanarwar da Femi Adesina ya fitar, Buhari ya sanar da hakan a ranar Alhamis a sansanin sojin sama da ke Maiduguri, jihar Borno.

TheCable ta ruwaito yadda mayakan ta'addancin ISWAP suka harba roka a Maiduguri kafin ziyarar Buhari domin kaddamar da wasu ayyuka a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng