Asirin kuɗi zan yi da shi: Malamin da aka kama da sabon ƙoƙon kan mutum da ya siya N60,000
- Jami'an yan sanda a jihar Ondo sun yi ram da wani da ya kira kansa malamin addinin musulunci mai suna Alfa Tunde Olayiwola da sabon kokon kan dan adam.
- Alfa Olayiwola ya amsa cewa ya biya wani mutum da suka hadu a wurin taro N60,000 ne don ya kawo masa kan har gida a nan ne yan sanda suka cafke shi.
- Malamin mai shekaru 55 a duniya ya ce yana son ya yi amfani da kokon kan ne domin yin asirin kudi don ya sauya rayuwarsa ya rika cabawa kamar attajiri
Ondo - Wani wanda ya kira kansa malamin addinin musulunci mai shekaru 55, Tunde Olayiwola, ya amsa cewa ya siyo sabon kokon kan dan adama a Ajabbale, Oka a jihar Ondo, Vanguard ta ruwaito.
Olayiwola, wanda yan sanda na jihar Ondo suka yi holensa ya ce ya siyo kan bil adaman ne domin a yi masa asirin kudi.
A hirar da ka yi da shi, wanda ake zargin da ya ce shi dan asalin garin Osogbo ne a jihar Osun, ya ce ya siya kokon kan ne kan kudi N60,000 domin a masa asiri, rahoton Blueprint.
Ya ce:
"Wani mutum da muka hadu a wurin taro ne ya kawo min kan har gida na a safiyar ranar Alhamis. Ina kokarin fara yin asirin ne a yayin da jami'an yan sanda suka kama ni.
"Na bukaci a kawo min kan dan adam ne domin in kyautata rayuwata kuma aka kawo min.
"Wannan shine karo na farko, amma ina son in yi arziki ne domin in yi rayuwa mai dadi. Ayau aka kawo min kokon kan."
Mun kama shi ne bayan samun bayanan sirri, Yan Sanda
Da ya ke magana kan lamarin, kwamishinan yan sandan jihar Ondo, Oyeyemi Oyediran ya ce:
"Jami'an yan sanda sun kama wanda ake zargin ne sakamakon bayanan sirri da suka nuna cewa yana daf da karbar wani sako."
Oyediran ya kara da cewa:
"An kama wanda ake zargin a lokacin da aka kawo masa sabon kokon kan kuma ya amsa cewa yana da niyyar yin asiri da kan ne domin ya inganta rayuwarsa."
Ya ce:
"A ranar 23 ga watan Disamban 2021, misalin karfe 9 na safe, yan sanda sun samu bayani cewa wani da ke kiran kansa malami mai suna Alfa Tunde Olayiwola, wani da ake zargin mai tsafi ne yana dab da karba sako da ake zargi kan dan adam ne."
An kama ɗan shekara 55 da ƙoƙon kan ɗan adam hudu
A wani labarin mai alaka da wannan, Rundunar yan sandan jihar Ogun ta kama wani dan shekara 55, Yesiru Salisu da laifin mallakar sassan dan adam da suka hada da kokon kai guda hudu, busassun hannaye biyu da muka muƙi guda uku kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
A wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyayemi ya fitar, kama wanda ake zargin ya biyo bayan wani rahoto da aka shigar a ofishin yan sanda na Ago Iwoye.
Mai magana da yawun rundunar ya bayyana cewa, rahotannin sun bayyana cewa an ga wanda ake zargin da jakar da ake zargin kayan sata ne, kuma da aka tambaye shi meye a jakar, sai ya yar da jakar ya gudu jeji.
Asali: Legit.ng