Sabon rikici: Bayan cire shi cikin 'yan takara, dan takarar APC a Anambra ya magantu
- Dan takarar gwamnan jihar Anambra a zaben 2021 na jam'iyyar APC ya bayyana cewa shi sam bai amince da hukuncin kotu ba
- A cewar kungiyar gangamin zabensa, dan takarar na APC zai daukaka kara kuma yana sa ran samun adalci a can
- A yau ne dai kotu ta soke kasancewarsa cikin 'yan takarar gwamna a zaben na Anmabra, lamarin da bai masa dadi ba
Abuja - Dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Anambra a ranar 6 ga watan Nuwamba, Sanata Andy Uba, ya yi watsi da hukuncin da mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya ya yanke wanda ya soke takararsa a matsayin dan takaran APC.
A wata sanarwa da mataimakin daraktan kungiyar yakin neman zaben Sanata Andy Uba (SAUGCO), Ikechukwu Emeka Onyia ya fitar, ya ce Andy Uba zai daukaka kara kan hukuncin, Daily Trust ta ruwaito.
Daya daga cikin masu neman takarar gwamna a jam’iyyar APC, George Moghalu, ya maka Andy Uba da jam’iyyar a kotu yana kalubalantarsu kan magudi a zaben fidda gwani na jam'iyyar.
A yau Litinin 20 ga watan Disamba ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke kasancewar Sanata Andy Uba a zaben gwamnan jihar Anambra, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Alkalin kotun ya ce wanda ya shigar da karar, George Moghalu, ya yi nasarar tabbatar da cewa jam’iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba wanda Uba ya yi ikirarin cewa ya lashe a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Alkalin kotun ya umarci INEC da ta goge sunan Uba daga jerin 'yan takarar zaben na Anmabra a tarihinta, The Nation ta ruwaito.
Biyo bayan hukuncin, Uba ya ce duk wani abu da za a fuskanta yana da yakinin cewa zai samu adalci a kotun daukaka kara.
Wa'adin shigar da kara ya kusa karewa, APC ba ta shigar da kara ba
A wani labarin, Daily Trust ta ruwaito cewa, saura kwanaki shida a cika wa’adin gabatar da kara domin kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra, kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar ba ta karbi batun ba daga wata jam'iyya ba har yanzu.
A cewar dokar, ‘yan takara da jam’iyyunsu da suka sha kaye suna da hurumin kwanaki 21 daga ranar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da zabe domin su gabatar da kara.
A ranar 10 ga watan Nuwamba ne jami’ar kula da zabe na jihar Anambra, Farfesa Florence Obi, ta ayyana Farfesa Charles Soludo na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaben.
Asali: Legit.ng