An Maka Kamfanonin Sadarwa Da Gwamna Matawalle a Kotu Kan Toshe Sabis a Zamfara
- Wata kungiya a Jihar Zamfara ta yi karar kamfanonin sadarwa da ke Najeriya kan dauke musu sabis wanda hakan ya janyo musu asara da wahalhalu
- Kungiyar ta bukaci babban kotun Jihar Zamfara ta duba yiwuwar biyansu diyya kan asarar da suka yi sakamakon karya kwantiragi na basu sabis da kamfanonin suka yi
- Har wa yau cikin wadanda aka yi karar har da Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari'ar Zamfara da Hukumar NCC
Zamfara - Wata kungiya a jihar Zamfara, mai suna 'Zamfara Cycle Community Initiative', ta shigar da kara a babban kotun Jihar Zamfara kan zargin saba ka'idar kwantiragi tsakanin kamfanin sadarwa da masu amfani da layukan waya a jihar.
Sun yi ikirarin cewa toshe hanyoyin sadarwa da aka yi a jihar na tsawon lokaci ya janyo wa mutanen jihar wahalhalu da asara kuma suna son kotun ta duba ko ya kamata a biya masu karar diyya saboda asarar da suka yi, rahoton Daily Trust.
Kamfanonin Sadarwan Ba su Nemi Izini Daga Kotu Ba, Masu Kara
Sun ce wadanda aka yi karar dukkansu suka toshe hanyoyin sadarwa a Jihar ta Zamfara tun 3 ga watan Satumban 2021 kuma bata nemi izinin yin hakan ba daga kotu.
Kawo yanzu, shida cikin kananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara ba su da sabis kamar yadda ya zo a rahoton na Daily Trust.
A cikin karar da suka shigar a kotun a ranar Litinin a Gusau, masu karar, Musa Umar da Ahmed Jamilu sun ci suna neman a biya su diyyar ne kan karya ka'aidar kwantiragi tsakanin Jihar da wadanda aka yi kara, MTN Nig. Communication Ltd., Globacom Ltd. da Bharti Airtel Ltd, don samar musu sabis na kira, imel da intanet.
Hakazalika, cikin wadanda aka yi karar har da Mai girma gwamnan Jihar Zamfara, Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari'a na Jihar Zamfara da Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC.
Masu shigar da karar sun dogara ne da wasu sassa na kundin shari'ar jihar Zamfara da suka hada da Order 15 Rule 3 (1) of the High Court of Zamfara State (Civil Procedure) Rules 2014, sections 96, 97, 98 da 99 na Sherriff and civil process Act, Cap 551, LFL 2004.
Rubutu a Facebook: Kotu ta bada belin hadimin Goje bayan tsare shi tsawon kwana 20
A wani labarin, alkalin wata Kotun Majistare da ke jihar Gombe ya bayar da belin sabon hadimin Sanata Muhammad Danjuma Goje a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.
Yayari ya na hannun ‘yan sanda tun ranar 30 ga watan Nuwamba bayan yin wata wallafa a shafinsa kan murabus din wasu masu makamai a jami’iyyar APC daga karamar hukumar Yamaltu/Deba.
Lauya mai kara, Barista Ramatu Ibrahim Hassan, ta sanar da kotu yadda wanda ake zargin a ranar 25 ga watan Nuwamban 2021 ya yi wata wallafa ta bogi akan wasu masu mukami a jam’iyyar APC a karamar hukumar Yamaltu/ Deba a shafinsa na Facebook.
Asali: Legit.ng