Bishop Kukah: Allah bai yi kuskure ba da ya halicci mutane masu addinai da ƙabilu daban-daban a Najeriya
- Matthew Kukah, fitaccen faston cocin Katolika da ke jihar Sokoto, ya ce Ubangiji bai yi kuskure ba da ya yi Najeriya a kasa daya tare da kabilu daban-daban
- A ranar Lahadi yayin bikin cikar shekarunsa 45 a matsayin fasto, kuma shekaru 10 a matsayinsa na Bishop din shiyyar jihar Sokoto, Kukah ya yi wannan furucin
- Yayin taron ya ce bacin taimakon iyayensa da cocinsu ba, da bai zama babban mai wa’azi ba inda ya bukaci ‘yan Najeriya su dinga alfaharin kasancewarsu ‘yan kasa
Jihar Sokoto - Matthew Kukah, faston cocin Katolika na shiyyar jihar, ya ce Ubangiji bai yi kuskure ba da ya yi Najeriya a matsayin kasa daya mai mabanbantan mutane ba, The Cable ta ruwaito.
Kukah ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin shagalin bikin cikarsa shekaru 45 a matsayin fasto da kuma shekaru 10 a matsayin Bishop na shiyyar Sokoto.
Yayin jawabi ga taron jama’a, Bishop din ya ce in banda kokarin iyayensa da cocinsu, da bai zama Bishop ba yayin da ya bukaci taron da su kasance masu tuna cewa duk wani abu a rayuwarsu kyautar Ubangiji ne.
Ya ci gaba da rokon ‘yan Najeriya akan su kasance masu alfahari da kasarsu a ko wanne lokaci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ubangiji bai yi kuskure ba da ya dunkule mu wuri guda
Kamar yadda ya ce:
“Ubangiji bai yi kuskure ba da ya yi mu a kasa guda tare da al’adu, addinai da yaruka daban-daban ba.
“Idan ina magana akan Najeriya, ina yi ne cike da alfahari saboda a gaban idanunmu Ubangiji zai bunkasa kasar yayin da za mu yi murnar tare.”
A lokuta da dama Kukah ya na nuna yardarsa akan ‘yan Najeriya su kasance a dunkule wuri guda.
Bishop din ya taba cewa zaman tare ya fi arha da rabuwar kawuna
A farkon shekarar nan Bishop din ya ce ya fi sauki ga Najeriya ta dunkule wuri daya akan a raba kawuna daban-daban.
Ya kara da cewa duk masu son a raba kasa su na da gaskiya idan ka duba nasu dalilan.
A watannin da su ka gabata, Kukah ya ce babu wanda zai ci nasara akan komai idan aka raba Najeriya.
Babu wanda zai amfana idan kasa ta rabu
Kamar yadda ya furta:
“Ba na tunanin akwai dan Najeriya mai hankalin da zai ce babu alakar da ta hada mu wuri guda. Amma na san kowa ya na da damuwarsa akan kasar nan.
“Ba za mu ci gaba da kasancewa a haka ba babu wani ci gaba, don haka babu wanda zai karu idan aka raba kasar nan, na san babu mai son kasar ta rabu.”
Sultan: Allah bai yi kuskure ba da ya haɗa mu zama tare a matsayin ƴan Nigeria
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar na III, ya bukaci dukkan kabilun Nigeria su cigaba da zama a matsayin yan uwan juna domin Allah bai yi kuskure ba da ya hada mu zama a matsayin kasa daya, Daily Trust ta ruwaito.
Da ya ke jawabi a matsayinsa na shugaba a wurin taron bada lambar yabo na shugabanci na 2020 a ranr Alhamis a Abuja, Sultan ya ce raba kasar ba zai magance matsalolin da kowace kabilar ke fama da shi ba amma hada kai tare a warware matsalar ce ta fi amfani.
Asali: Legit.ng