Wata sabuwa: Kotu ta soke kasancewar dan takarar APC a zaben gwamnan Anambra
- Kotun da ke zama a babban birnin tarayya Abuja ta soke kasancewar Sanata Andy Uba cikin 'yan takarar gwamnan Anambra
- Wannan ya biyo bayan karar da wani dan jam'iyyarsu ta APC ya shigar kan rashin gaskiya a zaben fidda gwani
- Alkali ya yanke wannan hukuncin ne a yau Litinin 20 ga watan Disamba, 2021 tare da ba INEC wani umarnin
Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke kasancewar Sanata Andy Uba a zaben gwamnan jihar Anambra da aka yi ranar 6 ga watan Nuwamba.
Mai shari’a Inyang Ekwo, a wani hukunci da ya yanke ranar Litinin, ya ce Uba dama bai zama dan takara ba a zaben bayan saboda ya fito daga zaben fidda gwani da jam’iyyar APC ta gudanar ba bisa ka’ida ba.
Alkalin kotun ya ce wanda ya shigar da karar, George Moghalu, ya yi nasarar tabbatar da cewa jam’iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba wanda Uba ya yi ikirarin cewa ya lashe a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Alkalin kotun ya umarci INEC da ta goge sunan Uba daga jerin 'yan takarar zaben na Anmabra a tarihinta, The Nation ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga nan sai ya umarci jam’iyyar APC da ta mayar wa mai kara kudi N22,500,000 da ya biya domin nuna sha’awa da sayen fom na tsayawa takara tunda jam’iyyar ta gaza wajen gudanar da sahihin zaben fidda gwani.
Wannan lamari dai na iya zama bangaren nasara ga Charles Soludo, wanda ya lashe zaben da ya gudana kuma dan jam'iyyar APGA.
Kotu ta kori karar da ke neman soke takarar gwamna na Soludo a Anambra
Idan baku manta ba, gidan talabijin na TVC ya ruwaito cewa, kotu ta yi watsi da karar da ta nemi a soke takarar gwamna da mataimakan gwamna na jam’iyyar APGA a zaben gwamnan da ya gabata a jihar Anambra.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, karar an shigar da ita kan dan takarar APGA da ya lashe zabe, Charles Soldu da mataimakinsa Onyeka Ibezim.
Masu shigar da kara – Adindu Valentine da Egwudike Chukwuebuka – suna zargin Soludo da Ibezim sun bayar da bayanan karya a cikin takardar da suka mika wa hukumar INEC don haka a bayyana cewa ba su cancanci tsayawa takara ba.
A wani labarin, Daily Trust ta ruwaito cewa, saura kwanaki shida a cika wa’adin gabatar da kara domin kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra, kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar ba ta karbi batun ba daga wata jam'iyya ba har yanzu.
A cewar dokar, ‘yan takara da jam’iyyunsu da suka sha kaye suna da hurumin kwanaki 21 daga ranar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da zabe domin su gabatar da kara.
A ranar 10 ga watan Nuwamba ne jami’ar kula da zabe na jihar Anambra, Farfesa Florence Obi, ta ayyana Farfesa Charles Soludo na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaben.
Asali: Legit.ng