Wata Sabuwa: An gurfanar da tsohon gwamna kan kin bayyana neman takarar shugaban kasa a 2023
- Wasu mutum biyu a jihar Bauchi sun gurfanar da tsohon gwamnan Abia, Orji Kalu a gaban kotu kan ya ki fara shirin takarar shugaban ƙasa a 2023
- Masu shigar da karan sun bukaci babbar kotun Bauchi ta tilasta wa sanatan ya nemi tikitin takara karkashin kowace jam'iyya
- A cewarsu Kalu na da kwarewa da zai ceto Najeriya daga halin ƙaƙani kayi da take ciki
Bauchi - Mutum biyu a jihar Bauchi sun shigar da ƙarar tsohon gwamnan jihar Abia, Chief Orji Uzor Kalu, gaban babbar kotun jihar Bauchi.
Tribune Online ta rahoto cewa masu shigar da ƙaran sun ɗauki wannan matakin ne bisa ƙin bayyana sha'awar takarar shugaban ƙasa a 2023 karkashin kowace jam'iyyar siyasa da ya yi.
Kwamaret Aliyu Ladan da Lawan Abdullahi, sune suƙa shigar da ƙarar gaban kotu, wadda mai shari'a, Mohammed Sambo, ke jagoranta.
Mutanen biyu sun bukaci kotu ta samar da wani umarni da zai tilastawa sanatan mai ci, Sanata Kalu, ya shiga jerin masu neman zama shugaban ƙasa a 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Meyasa suka maka shi a kotu?
Yayin da suke zantawa da manema labarai a ƙarshen mako, masu shigar da ƙara sun bayyana cewa sun maka Kalu gaban kotu ne saboda suna tsammanin shi kaɗai ne zai iya ceto Najeriya daga halin da take ciki.
Sun ƙara da cewa Najeriya ta faɗa cikin rikici kuma yan Najeeiya na fama da yanayi, bisa haka mutum mai hangen nesa kamar Kalu ne kaɗai zai iya ceto ƙasar.
A cewarsu:
"Mun san zai iya canza yanayin nan, yana da kwarewar canza abu, daga ba dai-dai ba zuwa abinda ya dace. Ya yi mun gani a jihar Abia duk da ƙalubalen da ake ciki."
"Mun zo kotu ne saboda muna son ta umarce shi ya girmama yarjejeniyar mu, ya nemi kujerar shugaban ƙasa. Muna son kotu ta tilasta wa Kalu ya ayyana sha'awar takara karkashin APC ko a kowace jam'iyya."
"Muna son kotu ta sa shi ya fara shiri tun yanzu kuma ya bi dukkan matakai domin neman tikicin takara a 2023."
A wani labarin na daban kuma Manyan jiga-jigan PDP da daruruwan mambobi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki
Jiga-jigan PDP tare da dandazon magoya bayansu daga mazaɓar sanata ta kudancin jihar Cross Ribas sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ranar Alhamis.
Gwamnan jihar Ben Ayade, yace babu kowa a jam'iyyar PDP ta jihar, tsagin adawa ya mutu murus.
Asali: Legit.ng