Wata sabuwa: 'Yan fashi da makami sun kai farmaki gidaje a Kano
- Wasu gungun 'yan fashi da makami sun farmaki wani yankin jihar Kano inda suka so aikata mummunan aiki
- Wani mazaunin yankin ya bayyana lamarin ya faru inda yace sun balle kofar gidan wani mutum domin su kutsa gidansa
- Allah ya kare faruwar lamarin, domin an kira 'yan sanda kuma sun zo cikin gaggawa domin daukar mataki
Kano - Wasu gungun ‘yan fashi da makami, a ranar Asabar, sun kai hari a unguwar Sabon Gari da ke kan hanyar Cakwaya, a karamar hukumar Rano ta jihar Kano.
Wani mutum a Facebook ya bayyana fargaba a Kano lokacin da ya wallafa cewa gungun ‘yan fashin a kwanaki kadan bayan rahotannin tsaro sun nuna cewa ‘yan bindigar da ke aiki a wasu jihohin Arewa maso Yamma na kutsa kai cikin Kano.
Sai dai wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na safe lokacin da ‘yan fashin suka kai farmaki yankin da muggan makamai kuma suka yi ta barna har zuwa karfe 4:00 na safe.
Ya ce sun kai hari gidan wani Auwalu Rabiu da ke sayar da wayoyi da kayan masarufi a tsakiyar kasuwar garin.
A cewarsa:
“Sun fi mutum 20 kuma kai tsaye suka wuce gidansa. Wuri ne na zama wanda muke kira Sabon Gari saboda yanzu yake tasowa.
“Sun buga kofa sau da yawa amma bai bude musu ba. Daga baya wani ya kira ‘yan sanda, nan take ‘yan sandan suka iso, sai ‘yan fashin suka gudu."
Rabiu, wanda aka kai wa hari a gidansa, ya ce ko da yake bai gansu ba, suna da yawa dauke da muggan makamai, kuma sun yi nasarar karya kofar gidansa.
A cewarsa:
“Sun buga amma ban bude ba daga baya suka karya kofar, amma dai ba su iya bude wata kofar da za ta bar su su shiga gidana ba.
“Kusan mintuna 20 suka kwashe suna kwankwasawa, daga baya da suka ji cewa ‘yan sanda na zuwa sai suka gudu.
“Ba su gaya mani komai ba kuma lokacin da ‘yan sanda suka zo, suka tafi. Sun bincika ko'ina da kewaye amma ba su ga komai ba."
Wata majiya daga wajen Sarkin Rano ta ce an kai musu rahoton lamarin, inda ta kara da cewa sarki ya umarci rundunar ‘yan sanda da ke yankin da ta binciki lamarin.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yi alkawarin tuntubar ‘yan sandan yankin na Rano domin tabbatar da batun.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto Kyawa bai ce komai ba.
Tun a watan Yuni gwamna Ganduje ke kira da a sa ido kan yankuna daban-daban a jihar Kano, domin ana zargin shigowar mabarnata musamman a dazukan jihar, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Jihar Kano na daga cikin jihohin da ke saukin hare-haren ta'addanci a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada
A wani labarin, a ranar Asabar din da ta gabata ne wasu mutane dauke da makamai suka yi garkuwa da babban limamin masarautar Owerri, Reginald Ejiogu, a karamar hukumar Owerri ta jihar Imo.
An yi garkuwa da Ejiogu ne tare da shugaban kauyen Umunwagbara na masarautar Owerri Nchi-Ise, Sunny Unachukwu.
Lamarin da wakilin jaridar Daily Trust ya tattaro ya faru ne da yammacin ranar 18 ga watan Disamba, 2021.
Asali: Legit.ng