Nasrun Minallah: Soji sun nakasa Turji, sun halaka 'yan bindiga a Zamfara da Sokoto
- A halin yanzu, shugaban 'yan bindigan Zamfara da Sokoto, Bello Turji, ya nakasa sakamakon miyagun raunikan da ya samu a samamen da soji suka kai maboyarsa
- Ba a nan sojojin Najeriyan suka tsaya ba, sun kai samame sansanonin 'yan bindiga da ke garuruwan Isam Sabon birni da gabashin Tozei
- Wasu daga cikin 'yan bindigan sun tsere da miyagun raunika tare da basu wasu makamansu amma sojin kasa sun bii su tare da mitsike su
Jihohin Zamfara da Sokoto - Fitaccen gagararren dan bindiga, Bello Turji, a halin yanzu ya nakasa sakamakon miyagun raunikan da ya samu yayin da jiragen yakin soji suka kai farmaki maboyarsu da wasu sansanonin 'yan bindiga da ke arewa maso yamma.
Jiragen yakin sojin saman na rundunar Operation Hadin Kai, ya kashe 'yan bindiga masu yawa a samamen da suka kai dajikan jihohin Zamfara da na Sokoto a safiyar Asabar, Leadership ta ruwaito.
Wata majiyar sirri ta sojojin Najeriya ta sanar da PRNigeria cewa, luguden ruwan wutan ta sama wanda aka hada da luguden sojin kasa, an yi shi ne a garin Shinkafi na jihar Zamfara da kuma Bafarawa da ke garin Sabon Birni a jihar Sokoto.
Kamar yadda majiyar sirrin ta bayyana, har yanzu ba a san yawan 'yan bindigan da aka sheke ba a samamen asubahin da suka kai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
PRNigeria ta tattaro cewa, wasu daga cikin 'yan bindigan da suka samu miyagun raunika sun yi kokarin tserewa amma sojin kasa sun yi musu kwanton bauna.
"Bayan ayyukan kawar da 'yan ta'addan da aka yi a jihohin Katsina da Zamfara daga ranakun 16-17 ga watan Disamba, sojin sun yi lugude da jiragen yaki a sansanonin 'yan bindiga da ke Sabon Birni, Isa da gabashin Tozei inda aka kashe 'yan bindiga masu yawa yayin da wasu suka tsere.
“Har ila yau, a safiyar 18 ga watan Disamba, sojin saman sun yi luguden wuta a kauyen Gebe da ke jihar Sokoto inda 'yan bindigan ke ta hantarar mutane amma sojin suka ragargajesu.
"A wurin, 'yan bindiga marasa yawa ne suka tsere inda suka bar makamansu," majiyar tace.
Mawaki ya gwangwaje shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, da wakar yabo da jinjina
A wani labari na daban, wata waka ta kwarzantawa tare da yaba wa fitaccen dan bindiga, Bello Turji, tana yawo a halin yanzu a arewacin Najeriya cikin mutanen da suke fama da cin zarafi tare da rashin kwanciyar hankalin da 'yan bindigan suke saka yankin.
Turji, wanda dan asalin garin Shinkafi ne daga jihar Zamfara, shi ne shugaban 'yan ta'addan da ke addabar jihohin Sokoto, Zamfara da wani sashi na jamhuriyar Nijar.
'Yan ta'addan ke da alhakin kisa da hana daruruwan jama'a sakat a yankin, Premium Times ta ruwaito.
Asali: Legit.ng