Rashin Tausayi: Asirin wasu ma'aurata da suka siyar da jariri dan wata daya ya tonu

Rashin Tausayi: Asirin wasu ma'aurata da suka siyar da jariri dan wata daya ya tonu

  • Dubun wasu ma'aurata mata miji da suka siyar da jariri ɗan wata ɗaya ya cika a jihar Ogun
  • Jami'an hukumar yan sanda reshen jihar sun yi ram da ma'auratan, waɗan da suka karbi N50,000 suka mika jaririn su
  • Kwamishinan yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya umarci jami'ai su tsananta bincike kan lamarin

Ogun - Jami'an hukumar yan sanda reshen jihar Ogun sun yi ram da wasu ma'aurata bisa zargin siyar da jaririn da suka haifa ɗan wata ɗaya.

Punch ta ruwaito cewa ma'auratan mata da miji, sun siyar da jaririn ne kan kuɗi naira dubu N50,000.

Ma'auratan, Eze Onyebuchi, da matarsa Oluchi Eze, suna zaune ne a layin Ayegbami dake yankin Ilara, ƙaramar hukumar Remo ta arewa, jihar Ogun.

Jihar Ogun
Rashin Tausayi: Asirin wasu ma'aurata da suka siyar da jariri dan wata daya ya tonu Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar, Abimbola Oyeyemi, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

Oyeyemi yace jami'an yan sanda sun damke mutanen da ake zargin ne bayan samu wasu bayanai da suka yi a hedkwatar yan sanda ta Ode-Remo.

Meyasa suka siyar da jaririn su?

Kakakin yan sandan yace ma'auratan sun siyar da jaririn bisa ra'ayin kansu ga wata mata da har yanzun ba'a gano ta ba.

Channels tv ta rahoto Oyeyemi yace:

"Bayan samun bayanai, shugaban caji ofis din Ode-Remo ya umarci jami'ai suka je yankin kuma suka taso ƙeyar ma'autan zuwa ofis."
"Yayin bincike ma'auratan sun sun shaida wa yan sanda cewa wata mai suna Ruth Obajimi ce ta musu kwatancen wacce zata siya jaririn, wacce har yanzun babu wanda ya san ta."
"Sun ce matar ta zo gare su ranar 14 ga watan Disamba kuma ta faɗa musu daga ofishin kare hakkin ɗan adam take, zata taimaka musu rabuwa da jaririn."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe dan Bijilanti, sun yi awon gaba da DSS a Abuja

"Matar ta ba su kudi N50,000 kuma suka damka mata yaron duk da cewa ba su san daga inda take ba. Jami'ai na cigaba kokarin nemo matar domin kubutar da jaririn."

Kwamishina ya bada umarni

Oyeyemi yace kwamishinan yan sandan Ogun, Lanre Bankole, ya umarci a maida lamarin sashin yaki da safarar mutane domin cigaba da bincike.

Kazalika kwamishinan ya sake baiwa jami'ai umarnin su bazama neman matar da ta siya, wacce ake tsammanin da bi wani jirgi ta fece.

A wani labarin kuma Muhimman abubuwa hudu da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhu

Jagoran yan bindiga, wanda ake ganin ya addabi jihar Zamfara da wasu yankuna, Bello Turji, ya nemi a zauna zaman sulhu

A ciki wasikar da ya aike wa shugaba Buhari, gwamna Matawalle, da sarkin Shinkafi, Turji ya nemi a cika wasu sharuɗɗa 4.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262