Innalillahi: 'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun hallaka mutane tare da kone gonakai

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun hallaka mutane tare da kone gonakai

  • Hukumomin tsaro a jihar Kaduna su mika rahoton hallaka mutane sama da 20 a wasu yankunan jihar
  • Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya karbi rahoton, inda ya bayyana jimaminsa kan wannan lamari
  • Ya kuma ba da umarnin fara binciko iyalan wadanda lamarin ya shafa domin baau agajin gaggawa daga gwamnati

Kaduna - Hukumomin sojan Najeriya da ‘yan sandan Najeriya sun kai wa gwamnatin jihar Kaduna rahoton cewa an kashe mutane sama da 20 a harin da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyukan karamar hukumar Giwa a jihar.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ‘yan bindiga sun kai hari kauyukan Kauran Fawa, Marke da Riheya da ke Idasu a karamar hukumar Giwa, inda suka kashe mutane sama da 20.

Kara karanta wannan

Rayuka 9 sun salwanta sakamakon farmakin da miyagu suka kai Kaduna

Kwamishinan tsaron Kaduna, Samuel Aruwa
Innalillahi: 'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun hallakamutane tare da kone gonakai | Hoto: Samuel Auwan
Asali: UGC

Ya ce an kuma kona gidaje, manyan motoci, da kananan motoci, tare da amfanin gona a gonaki daban-daban, Daily Nigerian ta ruwaito.

A cewar Aruwan:

“Gwamna Nasir El-Rufai ya karbi rahoton cikin bakin ciki tare da mika ta’aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su yayin da yake addu’ar Allah ya jikan su."

Ya ce gwamnan ya kuma jajanta wa al’ummar da abin ya shafa, ya kuma umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna da ta gudanar da aikin tantancewar cikin gaggawa a yankin domin bayar da agaji.

Ya kara da cewa:

“Za a buga sunayen wadanda aka kashe da zarar an tabbatar da karin bayani daga gwamnatin jihar Kaduna. A halin da ake ciki, jami’an tsaro suna ci gaba da sintiri a yankin gaba daya."

Kara karanta wannan

Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama

A makwannin da suka gabata an samu faruwar munanan hare a jihar Kaduna, lamarin da ya jawo mace-mace a jihar.

A jiya ne kwamishinan ya kuma tabbatar da hallaka wasu mutane tara a yankuna daban-daban na jihar kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin Arewa maso yammacin kasar nan da 'yan bindiga suka addaba a wannan shekarar.

Gwamnan APC ya gano masu daukar nauyin ta'addanci a jiharsa, ya saka ranar fallasa su

A wani labarin, Gwamna Hope Uzodimma ya sha alwashin bayyana sunayen wadanda ke da hannu wajen kai hare-hare a jihar Imo da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

PM News ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki da za a gudanar a ranar Litinin 3 ga watan Janairu, 2022.

Ya yi bayanin cewa wasu mutane 18 ne da jami’an tsaro suka kama kwanan nan kan kashe kansiloli biyu a jihar, sun bayyana sunayen wadanda suke haddasa rashin tsaro, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.