Dirarsa ke da wuya, Shugaba Buhari ya gana da Shugaban kasar Turkiyya
- Shugaba Buhari ya bazama aiki daga dirarsa birnin Istanbul, kasar Turkiyya da yaje ranar Alhamis
- Shugaban kasan ya dira babbar tashar jirgin birnin da daren Alhamis tare tawagar da suka taka masa baya
- Ya halarci muhimmin taro tare da sauran shugabannin kasashen Afrikan da zasu hallara
Turkey - Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, da safiyar Juma’a, 17 ga Disamba, 2021 a birnin Istanbul.
Hadimin Shugaban Kasan, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a hotunan da ya saki a shafinsa na Facebook.
Shugabannin kasashen biyu sun yi zaman diflomasiyya tare Istanbul.
Wannan ganawa ya faru ne bayan da ya dira tashar jirgin birnin Istanbul.
Buhari ya tafi Turkiyya halartan taron hadin kan kasar da Afrika
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu ya tafi Istanbul daga Abuja, don halartan taron hadin kan Turkiya da Afrika karo na uku, wanda Shugaban Recep Tayyip Ergogan, ya shirya."
Ana kyautata zaton wannan taro zai samar da hanyoyin habaka hadin kai tsakanin kasar da kasashen nahiyar Afrika a shekaru biyar masu zuwa.
Malam Garba Shehu, ya kara da cewa Shugaban kasan zai dawo Abuja ranar Lahadi, 19 ga Disamba.
Suwa suka bi shi
Shugaban kasan ya samu rakiyar manyan ministoci bakwai da ma'aikatan gwamnati sama da guda goma.
Sun hada da matarsa, Aisha Buhari; Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya); Ministan Abuja, Mohammed Bello da Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire.
Sauran sune Ministan Noma, Mohammed Abubakar; Ministan kasuwanci da masana'antu, Adeniyi Adebayo; NSA Babagana Monguno da Dirakta Janar na NIA, Ambasada Ahmed Rufa'i Abubakar.
Yaushe zai dawo?
Malam Garba Shehu, ya kara da cewa Shugaban kasan zai dawo Abuja ranar Lahadi, 19 ga Disamba.
Asali: Legit.ng