Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Istanbul, Kasar Turkiyya

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Istanbul, Kasar Turkiyya

Jirgin Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari da Hajiya Aisha, yanzu haka ya dira tashar jirgin birnin Istanbul, Kasar Turkiyya da daren Alhamis, 16 ga Disamba, 2021.

Hadimin Shugaban Kasan, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a hotunan da ya saki a shafinsa na Facebook.

Shugaban kasan ya samu rakiyar manyan ministoci bakwai da ma'aikatan gwamnati sama da guda goma.

Sun hada da matarsa, Aisha Buhari; Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya); Ministan Abuja, Mohammed Bello da Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire.

Sauran sune Ministan Noma, Mohammed Abubakar; Ministan kasuwanci da masana'antu, Adeniyi Adebayo; NSA Babagana Monguno da Dirakta Janar na NIA, Ambasada Ahmed Rufa'i Abubakar.

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Istanbul, Kasar Turkiyya
Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Istanbul, Kasar Turkiyya Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Jerin duka 'Yan tawagar Shugaba Buhari yayin da ya bar Najeriya zuwa taro a Turkiyya a yau

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Istanbul, Kasar Turkiyya
Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Istanbul, Kasar Turkiyya Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Taron da Buhari ya tafi halarta

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu ya tafi Istanbul daga Abuja, don halartan taron hadin kan Turkiya da Afrika karo na uku, wanda Shugaban Recep Tayyip Ergogan, ya shirya."

Ana kyautata zaton wannan taro zai samar da hanyoyin habaka hadin kai tsakanin kasar da kasashen nahiyar Afrika a shekaru biyar masu zuwa.

Malam Garba Shehu, ya kara da cewa Shugaban kasan zai dawo Abuja ranar Lahadi, 19 ga Disamba.

Ya bayyana a jawabin da ya saki da safiyar Alhamis.

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Istanbul, Kasar Turkiyya
Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Istanbul, Kasar Turkiyya Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Istanbul, Kasar Turkiyya
Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Istanbul, Kasar TurkiyyaHoto: Presidency
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel