Gwarazan yan sanda sun bindige ƙasurgumin ɗan bindiga har lahira, sun ceto mutane
- Jami'an yan sanda masu yaki da sace mutane sun hallaka wani jagoran yan bindiga bayan musayar wuta a Ebonyi
- Gwarazan yan sandan sun kuma samu nasarar ceto wata mata da yan bindigan suka sace da motarta
- Kwamishinan yan sanda na jihar Ebonyi, CP Aliyu Garba, ya umarci yan sanda su damko ragowar yan bindigan da suka tsere
Ebonyi - Rundunar yan sanda reshen jihar Ebonyi ta bayyana cewa jami'anta sun bindige wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai garkuwa, sun ceto wata mata Chukwu Felicia Nkechi.
Tribune Online ta rahoto cewa yan sandan sun garzaya da wacce suka samu nasarar ceto wa zuwa Asibiti domin duba lafiyarta.
Kakakin yan sanda jihar, DSP Loveth Odah, ita ce ta bayyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abakaliki ranar Alhamis.
Odah ta kara da cewa yan sandan sun kuma kwato motar wacce aka ceto da kuma wasu makamai a hannun yan bindigan.
Yadda yan sanda suka kashe ɗan bindigan
Kakakin yan sandan tace:
"Mun samu rahoton yan bindiga sun sace Chukwu Felicia Nkechi ranar 14 ga watan Disamba da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, a cikin motarta Toyota Corolla Car 2011 kan hanyar Nsugbe dake Abakaliki."
"Nan take jami'an yan sanda masu yaƙi da sace mutane suka fara aiki, suka gano maɓoyar yan bindigan a Layout Nkaliki, karamar hukumar Abakaliki, kuma suka dura wurin."
"Daga zuwan yan sandan, sai yan bindigan suka bude musu wuta, suma suka maida martani a akai ɗauki ba daɗi. Yayin haka ne suka bindige ɗaya daga cikin su wanda daga baya aka gano shi ne jagoran yan bindigan."
Odah ta kara da cewa jami'an yan sandan sun yi gaggawar kai ɗan bindigan asibiti domin ceto rayuwarsa amma daga baya likita ya tabbatar da ya mutu.
Shin ya sauran yan bindigan suka yi?
Kwamishinan yan sandan jihar, CP Aliyu Garba, ya umarci gwarazan yan sanda kada su zauna, su bi sawun ragowar yan bindigan da suka tsere.
Ya kuma jaddada kokarin hukumarsa na ganin ta kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar Ebonyi, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
A wani labarin na daban kuma Majalisa ta yanke hukunci kan yan majalisun da take zargi da alaka da yan bindiga a Zamfara
Kwamitin ɗa'a na majalisar dokokin jihar Zamfara ya gabatar da rahoton bincike kan mambobin da ake zargi suna da alaƙa da yan bindiga.
A zaman majalisar na ranar Laraba, ta umarci yan majlisun da abin ya shafa daga mazabun Anka da Bakura su cigaba da halartar zama.
Asali: Legit.ng