Majalisa ta yanke hukunci kan yan majalisun da take zargi da alaka da yan bindiga a Zamfara
- Kwamitin ɗa'a na majalisar dokokin jihar Zamfara ya gabatar da rahoton bincike kan mambobin da ake zargi suna da alaƙa da yan bindiga
- A zaman majalisar na ranar Laraba, ta umarci yan majlisun da abin ya shafa daga mazabun Anka da Bakura su cigaba da halartar zama
- Kakakin majalisa ya yaba wa kwamitin bisa jajircewa kan aikin da aka ɗora masa
Zamfara - Majalisar dokokin jihar Zamfara ta ɗauki matakin dawo da mambobinta guda biyu da ta dakatar a baya bisa zargin alaƙa da yan bindiga.
Premium Times tace yan majalisun sun ɗauki wannan matakin ne bayan amince wa da rahoton kwamitin ɗa'a, wanda ya gudanar da bincike a kai.
Yan majalisun biyu, Ibrahim Tudu-Tukur (Bakura) da Yusuf Anka (Anka) an dakatar da su ne a watan Oktoba bisa zargin suna da alaƙa da yan bindiga a yankunan da suke wakilta.
Mamban majalisar, Yusuf Kanoma, shi ne ya gabatar da kudiri kan dakatar da abokan aikinsa, inda ya yi zargin cewa Bakura da Anka, "Sun yi farin ciki da sace mahaifin kakakin majalisa, Marigayi Alhaji Mu’azu Magarya."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma yan majalisun biyu sun musanta wannan zargi, kuma daga baya suka ce dakatar da su yana da alaƙa da dambarwar siyasa.
An wanke su daga zargi
A zaman majalisar na ranar Laraba, shugaban kwamitin ɗa'a, Kabiru Dansadau, ya gabatar da rahoton bincike kan zargin.
Kwamitin a cikin rahotonsa ya wanke mambobin majalisan biyu daga zargin da ake musu na hannu a ayyukan yan bindiga a yankunan su.
Wani mamba a majalisar daga yammacin Zamfara, wanda ya nemi mu boye sunansa, ya bayyana cewa an dawo da mutanen biyu sabida, "Babu wata hujja da ta tabbatar da abinda ake zarginsu."
Hakanan kuma ya shaida wa manema labarai cewa wasu daga cikin dattawan Zamfara sun sa baki kan lamarin, shiyasa aka dawo da su.
Majalisa ta tabbatar
Hadimin kakakin majalisar dokokin jihar, Mustapha Jafaru, ya tabbatar da cewa majalisa ta umarci su dawo bakin aiki amma ya musanta cewa wasu daga waje sun saka baki.
Punch ta rahoto shi yana cewa:
"Abin da zan iya cewa shine majalisa ta amince da shawarwarin kwamitinta. Kakaki ya yaba wa kwamitin bisa jajircewa a kan aikinsa ya kuma yaba wa yan majalisun bisa bin doka."
Kazalika yace yan majalisun da abin ya shafa za su cigaba da halartan zaman majalisa a shekara mai zuwa.
A wani labarin na daban kuma Rikici mai tsanani ya ɓarke tsakanin yan bindiga a jihohin Zamfara da Katsina
Rahotannin dake fitowa sun bayyana cewa an fara takun saƙa mai tsanani tsakanin yan bindigan Katsina da na Zamfara.
Wata majiya ta shaida cewa tawagar yan bindiga biyu sun hana baƙin yan bindiga shigowa yankunan su dake Batsari a Katsina.
Asali: Legit.ng