Shugaba Buhari ba zai iya magance matsalar tsaro a shekara mai zuwa ba, inji minista
- Alhaji Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu ya yi magana game da ayyukan 'yan fashi a gwamnatin Buhari
- A cewar ministan, babu wani shugaban kasa da zai iya cewa ko kuma bayyana lokacin da za a kawo karshen ta'addanci a kasar,
- Lai Mohammed da yake yaba kokarin da gwamnati da rundunar da ke yaki da rashin tsaro a kasar ke yi, ya kara da cewa ya kamata a ga kokarin gwamnatin Buhari
Abuja - Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya ce babu wani shugaban kasa da zai ce za a kawo karshen ayyukan ta’addanci a shekara mai zuwa.
Ministan, a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Laraba, 15 ga watan Disamba, ya amsa tambaya kan ko za a kawo karshen kalubalen tsaro a yanzu kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki a 2023, inji rahoton Daily Trust.
Alhaji Mohammed ya kuma yabawa hukumomin tsaro bisa ci gaba da yi wa kasa hidima.
Yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ba kowa, ban da tabbacin wani shugaban kasa da zai ce nan da shekara mai zuwa za a kawo karshen ‘yan bindiga. Kamar dai a ce zuwa shekara mai zuwa, ba za a samu barawo ba.
“Amma abin da ke da muhimmanci shi ne su yi mana hukunci ta hanyar duba nasarar da muka samu. Ba mu jefa hannayenmu cikin iska ba. Akwai lokacin da suka nemi mu dauki hayar sojojin waje, amma sojojinmu suna yin iya kokarinsu a cikin wannan yanayi.”
Ba dan Buhari ba da tuni Najeriya ta zama daular musulunci, inji Lai Mohammed
Hakazalika, ministan ya ce ba don ayyukan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, da ‘yan ta’adda sun alanta Najeriya a matsayin daular Musulunci.
Ya kara da cewa, ‘yan baya za su tuna alherin Buhari, wanda ya ce ya sanya tsaro ya zama babban abin da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai.
Ya ce a tarihin Najeriya babu wata gwamnati da ta baiwa jami’an tsaro kayan aikin da ake bukata domin magance matsalar rashin tsaro kamar na Buhari, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma bayyana cewa, tun farkon hawan shugaba Buhari a 2015, shugaban ya mayar da hankali kan kawo hanyoyin magance matsalar tsaro, inda yace hakan ba abin mamaki bane kasancewar yana cikin alkawuran Buhari guda uku.
Matasan Arewa ga Obasanjo: Kai dai ba ka da bakin sukar gwamnatin shugaba Buhari
A wani labarin, kungiyar matasan Arewa (NYA) ta ce tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba shi da halin da'a da har zai iya sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Obasanjo dai ya bayyana a wani taro a Abuja ranar Litinin, inda ya ce Buhari ya yi iya bakin kokarinsa da zai iya, kuma tsammanin ya kara yin wani abu kamar zaburar da mataccen doki ne.
Sai dai a wata sanarwa da mataimakin sakataren yada labaran NYA na kasa Mohammed Hussani Bauchi ya fitar, ya ce tara mutane domin sukar Buhari ba daidai bane.
Asali: Legit.ng