Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

  • A kwanakin baya wasu miyagun yan bindiga sun kashe mutane da dama suna tsaka da sallah a Maza Kuka ta jihar Neja
  • A halin yanzun jami'an tsaro sun kame shugaban tawagar yan bindigan da kuma wasu mambobinsa da zargin hannu a mummunan harin
  • Hukumar yan sandan jihar ta sanar da cewa ta kwato makamai a hannun su, kuma tana cigaba da bincike

Niger - Wasu daga cikin yan bindigan da suka kashe masallata 18 a ƙauyen Maza-Kuka, ƙaramar hukumar Mashegu, jihar Neja, sun shiga hannu.

Kwamishinan kananan hukumomi, cigaban karkara, harkokin naɗe-naɗe da tsaron cikin gida, Emmanuel Umar, shi ne ya sanar da haka yayin da yake bayani ga manema labarai a Minna ranar Laraba.

Daily Trust ta ruwaito kwamishinan na cewa ba zai iya bayyana adadin waɗan da suka shiga hannu ba a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Miyagun Yan bindiga sun kuma sace wani Sarki a Najeriya

Bajen yan sanda
Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mista Umar ya kara da cewa gwamna Abubakar Sani Bello, ya saka hannu kan dokar yan bijilanti domin taimaka wa wajen samar da tsaro a cikin gida

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin mutum nawa ne suka shiga hannu?

Sai dai da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, yace mutum 6 ne suka cafke da hannu a kisan wanda ya auku ranar 26 ga watan Oktoba, 2021.

Ya kuma bayyana sunayen su da; Mohammed lawali, Suleiman Ibrahim, Mohammed Rebo, Bashir Audu, Monsoru Abubakar da kuma Abubakar Hamidu.

Linda ikeji ta rahoto Kakakin yan sandan yace:

"A binciken da muka yi mun gano jagoran maharan, Muhammad Lawali, da kuma wasu daga cikin mambobin tawagar, sun tsero ne daga gidan gyaran hali na Lokoja."
"Mun kama Bashir Audu ne bisa laifin kaiwa yan bindigan miyagun kwayoyi. Mun kwato bindigun AK-47 biyu, jakar makamai da alburusai uku, da kuma wasu kwayoyi daga hannunnsu."

Kara karanta wannan

DSS ta ce jama'a su kula, ana kokarin fara daukar dalibai aikin bindiganci da sace mutane

A wani labarin na daban kuma Rikici mai tsanani ya ɓarke tsakanin yan bindiga a jihohin Zamfara da Katsina

Rahotannin dake fitowa sun bayyana cewa an fara takun saƙa mai tsanani tsakanin yan bindigan Katsina da na Zamfara.

Wata majiya ta shaida cewa tawagar yan bindiga biyu sun hana baƙin yan bindiga shigowa yankunan su dake Batsari a Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262