Jaruma Rahama Sadau ta caccaki gwamnatin Buhari kan hauhawar rashin tsaro

Jaruma Rahama Sadau ta caccaki gwamnatin Buhari kan hauhawar rashin tsaro

  • Jaruma Rahama Sadau ta caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan hauhawar kashe-kashen da arewacin Najeriya ke fuskanta
  • Jarumar ta bayyana yadda talaka baya zaman kwanciyar hankali a cikin gidansa balle waje, ta bukaci gwamnati ta dauka mataki kafin mutane su kai bango
  • A cewar jarumar, shugabannin mu basu da tausayi domin gwamnati ta nuna halin ko in kula kan abubuwa da ke faruwa a arewaci da kuma kasar baki daya

Fitacciyar jarumar fina-finai ta Najeriya, Rahama Sadau, ta caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ta gaza shawo kan matsalar tsaro da ta kazanta a arewa da Najeriya baki daya.

Sadau wacce ta wallafa caccakar a shafinta na Instagram a ranar Litinin, ta ce "har sai gwamnati ta tashi tsaye kan lamarin, ko kuma za a iya kai 'yan Najeriya bango har su yi bore".

Kara karanta wannan

Matasan Arewa ga Obasanjo: Kai dai ba ka da bakin sukar gwamnatin shugaba Buhari

Jaruma Rahama Sadau ta caccaki gwamnatin Buhari kan hauhawar rashin tsaro
Jaruma Rahama Sadau ta caccaki gwamnatin Buhari kan hauhawar rashin tsaro. Hoto daga BBC Hausa
Asali: UGC

Ta kara da kwatanta shugabannin Najeriya da "masu azabtarwa tare da rashin tausayi".

Wani sashi na wallafar ta ya ce, "Talakan Najeriya ba zai iya zama cikin gidansa hankali kwance ba, ya na rayuwa cikin tsoro. Idan duk aka kashe mu, sai mu ga wanda zai sake zaben ku."

Hauhawar rashin tsaro

Wallafar Sadau ta zo ne a yayin da kungiyoyin hadin kai tare da masu kishin Najeriya a ranar Talata suka balle zanga-zanga a garin Abuja.

Masu zanga-zangar suna bukatar a gaggauta dakile kashe-kashen da ke aukuwa a yankin.

Sun kara da jajanta yadda aka kashe fasinjoji arba'in a cikin bas a kauyen Gidan Bawa da ke jihar Sokoto ta hanyar babbaka su da ransu.

#JininArewanaKwarara ya dinga yawo a makon da ya gabata har zuwa yanzu. Ana ta kira ga fitattun mutane da kuma sanannu da a yi zanga-zanga kan halin ko in kula da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta nuna kan kashe-kashen da ake yi a yankin.

Kara karanta wannan

DSS ta ce jama'a su kula, ana kokarin fara daukar dalibai aikin bindiganci da sace mutane

Sarkin Musulmi ya ja kunne kan siyasantar da rashin tsaro, ya ce yunwa ba ta san addini ba

A wani labari na daban, Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar, ya ja kunne akan kada shugabannin addinai da 'yan siyasa su mayar da matsalar tsaron Najeriya ta siyasa.

Ana ta samun karin rashin tsaro, ta’addanci da sauran ayyukan assha yayin da ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda su ke cin karensu babu babbaka a arewa maso yamma, arewa maso gabas da sauran bangarori.

Akwai mutane da dama da aka halaka, aka yi garkuwa da su sannan wasu aka yi musu fyade, Channels TV ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel