Zuƙi ta malle: ASUU ta magantu kan ikirarin FG na bata N52.12bn

Zuƙi ta malle: ASUU ta magantu kan ikirarin FG na bata N52.12bn

  • Kungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’i, ASUU, ta musanta maganar ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige akan biyan kungiyar Naira biliyan 52.12
  • A cewar kungiyar, kalamansa na ha’inci da yaudara ne wadanda ya yi musamman don bata sunan kungiyar a idon jama’ar Najeriya
  • Yayin hira da manema labarai, mai gudanarwa na shiyar Kano na kungiyar, Kwamaret Abdulkadir Muhammad ya ce N22.17 ne kadai gwamnati ta saki

Kungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’i na kasa, ASUU ta musanta maganar ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, wanda ya ce N52.12b suka sakar wa kungiyar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar ta kwatanta maganarsa a matsayin kalaman yaudara da ha’inci wadanda ya furta musamman don bata kungiyar a idon jama’a.

Zuƙi ta malle: ASUU ta magantu kan ikirarin FG na bata N52.12bn
Zuƙi ta malle: ASUU ta magantu kan ikirarin FG na bata N52.12bn. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Yayin hira da manema labarai a ranar Laraba, mai gudunarwar kungiyar na shiyyar Kano, Kwamaret Abdulkadir Muhammad, ya ce N22.17b kadai gwamnati ta sakar wa kungiyar na alawus din ma’aikatan wanda a ciki 75% (N16.6bn) ne kadai na ‘yan kungiyar, yayin da sauran 25% din na sauran kungiyoyi ne.

Kara karanta wannan

Yanzu sai mun hada da noma da tuka motar haya, sannan mu koshi – ASUU tace gari ya yi zafi

A cewarsa, kungiyar ba ta jin dadin yadda gwamnati ta ke kokarin wanke idanunta a idon jama’an amma ta ke kokarin bata musu suna.

Ya kara da cewa yarjejeniyar da suka yi ita ce ta fi muhimmanci don kawo gyara akan matsalolin jami’o’in kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.

“A cikin N30b wanda cikin shi N20b ne aka sakar wa hukumar jami’o’i don kawo gyara a rubabbun gine-ginen cikin jami’o’i, ko kwabo ba za ta shiga asusun wani dan kungiyar ASUU ba.
“Yana da kyau kuma jama’a su kula da cewa ko N22.17b EEA da aka biya, kaso 75% ne kadai na kungiyar mu, sauran 25% na sauran kungiyoyin ne.
“Don haka muke kira ga minista da ya yi kokarin bayyana gaskiya, ya guji amfani da siyasa a bangarori masu muhimmanci a kasar nan kamar jami’o’in ilimi don a gina rayuwar shugabannin gobe na kasar mu,” a cewarsa.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya kara wani kaso mai tsoka a albashin 'yan sanda

Kungiyar ta yi kira ga gwamnati akan kawo karshen rashin tsaro, ta’addanci, garkuwa da mutane da kashe-kashen rayukan ‘yan Najeriyan da basu ji ba basu gani ba.

Ta kuma nuna rashin jin dadin ta akan yunkurin gwamnatin na kara haraji da cire tallafin man fetur wanda hakan zai azabtar da ‘yan Najeriya.

ASUU ta yi barazanar zuwa sabon yajin aiki, ta bawa gwamnati wa'adin sati 3

A wani labari na daban, kungiyar malaman jami’o’i na Najeriya ta ASUU ta bai wa gwamnatin tarayya makwanni 3 don cika mata sharuddan da ta gindaya wa gwamnatin, The Nation ta ruwaito.

Ta bayyana wannan kudirin nata ne inda ta ce wajibi ne gwamnatin ta cika mata alkawarran da su ka sa hannu akai tun ranar 23 ga watan Disamban 2020.

ASUU ta ce in har gwamnatin bata cika sharuddan na ta ba cikin makwanni 3 za ta dauki tsattsauran mataki.

Kara karanta wannan

Mala Buni na fuskantar barazana, Matasan APC sun nemi kotu ta tsige Shugaban Jam’iyya

Har ila yau kungiyar ta kafa kwamiti mai zaman kansa don bincike akan matsayin da aka bai wa ministan sadarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng