Daga karshe: Gumi ya bayyana bukatun 'yan bindiga 5 da FG za ta cika kafin su ajiye makamai
- Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, ya bayyana cewa akwai yadda gwamnatin tarayya za ta yi wa 'yan bindiga har su yadda makamansu baki daya
- A cewar shehin malamin addinin musulunci, 'yan bindigan na bukatar muhalli, makarantu, wurin kiwo, asibitoci da kuma wurin noma
- Malamin ya ce suna da mata tare da 'ya'ya kuma gwamnati ba ta taba tambayar yadda iyalan ke yi ba yayin da sojoji ke yi musu luguden wuta
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, ya bayyana cewa kasar nan tana fuskantar matsaloli masu yawa duk da dai tun can baya akwai matsaloli masu tarin yawa a kasar nan.
Shehin malamin ya yi magana kan matsalar tsaro inda yace akwai wadanda basu da aikin yi, akwai kuma 'yan Najeriya da ba su da ko shaidar kammala karatun firamare.
A cewar Gumi, a baya 'yan bindiga basu garkuwa da mutane domin su kashe su, suna garkuwa da mutane ne domin su samu kudi kawai, abun tamabaya a nan shine, me yasa suke kashe mutane? Menene ya sauya daga cikin al'amuransu har suke kashe mutane saboda jin dadinsu?
"Suna da mata su ma, suna da 'ya'ya kuma. Kun taba tsayawa kun tambaya abinda ke faruwa da 'ya'yansu idan ana musu luguden wuta? Kuna cewa sun sace yara 'yan makaranta, kun taba tambayar wacce makaranta 'ya'yansu ke zuwa?
"Da ace mun karbe su a matsayin 'yan Najeriya, suna samun abinda 'yan Najeriya suke samu, da babu shakka za mu ga sauyi," malamin yace.
Babban malamin ya ce ba koyaushe bane za a dinga kiran soja, soja ba, zaman lafiya ake so kuma ake fata. Ya ce ya ga cewa zaman lafiya za ta yi maganin wannan.
Kamar yadda ya bayyana yayin hira da Channels TV kuma Legit.ng ta kiyaye, ya ce:
"Abinda 'yan bindiga ke bukata shine a gina musu makarantu da muhalli, wurin kiwo, asibitoci da wurin noma. Wannan ne kacal ya dace a yi wa Fulani domin ganin sun mika makamai."
Sheikh Gumi ya bayyana yadda 'yan bindiga suka fi gwamnati son ganin karshen ta'addanci
A wani labari na daban, Sheikh Ahmed Gumi, shahararren malamin addinin Islama a Najeriya ya bayyana cewa, 'yan bindiga sun fi kaunar a kawo karshen ta'addanci fiye da gwamnati.
Malamin ya bayyana haka ne yayin wata hira da jaridar Daily Trust, inda ya bayyana kokarinsa na shawo kan 'yan bindiga domin su bar aikata barna su zauna da kowa lafiya.
Gumi ya daura laifukan da suke faruwa na rashin tsaro ga gwamtocin kasar nan, inda ya bayyana cewa, a cikinsu akwai wadanda suke amfana da tashe-tashen hankula shiyasa basa son batun ya kare.
Asali: Legit.ng