Da Dumi-Dumi: Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

Da Dumi-Dumi: Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

  • Tsohon gwamna Chukwuemeka Ezeife ya rasa matarsa, Njideka, wace ta rasu a baya-bayan nan bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Tsohuwar matar gwamnan na jihar Anambra ta rasu ne a wani asibiti da ke kasar Amurka duk da cewa ba a bayyana ciwon da ta ke fama da shi ba
  • Kamar yadda kungiyar dattawan Igbo suka bada rahoto, Njideka na shirin dawowa Najeriya ne a ranar Litinin 14 ga watan Disamba amma hakan bai yiwu ba

Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan da SSS suka fatattaki masu zanga-zanga a Katsina, Masari ya kai kara wajen Buhari

Da Dumi-Dumi: Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka
Matar tsohon gwamnan Najeriya ta rasu a asibitin Amurka. Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Sanarwar ta ce:

"Cike da alhini da tawakalli ga Allah, Na rubuta wannan sakon ne don sanar da dattawan Igbo rasuwar mai girma, Cif Mrs Njideka Ezeife, tsohuwar matar gwamnan Jihar Anambra kuma shugaban mu, Mai girma Dr Chukwuemeka Ezeife bayan gajeruwar rashin lafiya a kasar Amurka.
"Ana bukatar mambobin mu su jajantawa iyalan Ezeife su kuma saka su a addu'oinsu."

Shugabancin 2023: Za mu durƙusa har ƙasa don nema wa kudu maso gabas goyon bayan sauran yankuna, Ezeife

A wani labarin, kun ji cewa 'yan kabilar Ibo su na ta ayyuka tukuru don ganin sun samu damar mulkar kasa a shekarar 2023 da ke karatowa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Dan takarar gwamna ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hatsarin mota

Yayin da sanannu kuma manyan kasar nan su ke ci gaba da dagewa wurin ganin sun samu hadin kan sauran yankuna.

A ranar Asabar, 4 ga watan Disamba, tsohon gwamnan jihar Anambra, Chukwuemeka Ezeife, ya ce a shirye kudu maso gabas take da ta durkusa har kasa don neman goyon bayan sauran yankuna wurin samun damar shugabantar kasa a 2023, Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164