Umahi ga IPOB: Kun yi kadan, ba ku isa hana shugaban kasa ziyartar kudu maso gabas ba
- Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya ce 'yan awaren IPOB sun yi kadan kuma basu isa su hana shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa jihohin kudu maso yamma ba
- Kamar yadda gwamnan yace, wani sakarai ya makale a wani wuri yana tada fitina, duk me kukan rashin tsaron kudanci, ya fito bakin daga ya samar da tsaron
- Gwamnan ya yi fatali da rade-radin da ke yawo kan cewa zai koma tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP, ya ce zaman lafiya da kwanciyar hankalin APC ya wadatar da shi
Ebonyi - 'Yan awaren IPOB basu da karfin ikon hana shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyartar wata jihar yankin kudu maso gabas, cewar gwamnan jihar Ebonyi, Gwamna David Umahi ya sanar.
The Nation ta ruwaito cewa, ya sanar da hakan ne yayin jawabi kan maganar kakakin IPOB, Emma Powerful inda ya ja kunnen shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi watsi da shirin kai ziyara jihar Ebonyi.
Gwamnan ya bayyana rashin gamsuwarsa kan matsayar kungiyar yayin jawabin godiya a cocin gidan gwamnatin jihar a Ebonyi, The Nation ta ruwaito
Rahotanni sun bayyana yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar domin kaddamar da wasu ayyuka amma gwamnan ya bayyana cewa sun yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai hakura da ziyarar sai shekara mai zuwa.
Ya ce: "Na ga yadda wani batacce wanda ke kiran kansa da dan aware, ya ce ba su maraba da shugaban kasa a jihar Ebonyi.
"Ina Paris kuma na sanar da shugaban kasa cewa shugabannin kudu maso gabas za su so ya ziyarcesu kan batun zaman lafiya a yankin kuma na roke shi da ya dage zuwan zuwa shekara mai zuwa.
"Amma bana son sanar da mutane saboda ina son su cigaba da ayyukan su kamar shugaban kasan zai zo a wannan shekarar. Bani da tabbacin mutum uku zuwa hudu sun san da hakan, na bar wa kaina ne.
"Don haka shugaban kasa zai zo a lokacin da ya so zuwa. Wannan sakaran dan awaren IPOB ne. Idan ya isa, ya fito jihar Ebonyi, ya ga yadda zai samu kafar komawa inda ya fito.
"Wani zai zauna can a wani wuri ya dinga fadin shirme tare da batar da yaranmu suna kashe kawunansu. Amma shi da kan shi ba zai je filin daga ba.
"Duk wanda zai bude kazamin bakinsa yayi batun tsaro a kudu maso gabas, ya zo ya jagoranci yakin da kansa a jihar. Idan suna fadin shirmensu, ku yi burus da su. Wannan kasar ta Ubangiji ce."
Umahi ya kara da yin watsi da rahotannin da ke cewa ya na kokarin komawa jam'iyyar PDP.
Ya ce ya gamsu da zaman lafiyar jam'iyyar APC wacce ya koma a shekarar da ta gabata.
Gwamnan kudu ya ce IPOB ba su kai 'yan bindiga gurbata ba, ya shirya sasanci da su
A wani labari na daban, Okezie Ikpeazu, gwamnan jihar Abia, ya ce 'yan awaren Indigenous People of Biafra (IPOB) ba su kai 'yan bindigan arewa gurbacewa ba.
A yayin tattaunawa da jaridar Vanguard, gwamnan ya ce hanyar da ta fi dacewa a shawo kan matsalar masu tada kayar bayan shi ne gwamnatin tarayya ta tattauna da su.
Ya ce akwai sakon da IPOB ke kokarin aikawa kuma akwai bukatar kowa ya tsaya tsayin daka.
Asali: Legit.ng