Gwamnan kudu ya ce IPOB ba su kai 'yan bindiga gurbata ba, ya shirya sasanci da su

Gwamnan kudu ya ce IPOB ba su kai 'yan bindiga gurbata ba, ya shirya sasanci da su

  • Okezie Ikpeazu, gwamnan jihar Abia ya tabbatar da cewa a shirye ya ke da ya tattauna da 'yan awaren IPOB
  • A cewar gwamnan jihar Nnamdi Kanu, 'yan awaren IPOB ba su kai 'yan fashin dajin arewacin Najeriya gurbata ba
  • Gwamnan ya ce har yau dan kasa ya ke kallon Nnamdi Kanu kuma ya fi masu kwashe malamai da dalibai daga makarantu

Abia - Okezie Ikpeazu, gwamnan jihar Abia, ya ce 'yan awaren Indigenous People of Biafra (IPOB) ba su kai 'yan bindigan arewa gurbacewa ba.

A yayin tattaunawa da jaridar Vanguard, gwamnan ya ce hanyar da ta fi dacewa a shawo kan matsalar masu tada kayar bayan shi ne gwamnatin tarayya ta tattauna da su.

Ya ce akwai sakon da IPOB ke kokarin aikawa kuma akwai bukatar kowa ya tsaya tsayin daka.

Kara karanta wannan

Allah kadai zai iya daukar rayuwa ta: Tinubu ya gana da mukarrabansa

Gwamnan kudu ya ce IPOB ba su kai 'yan bindiga gurbata ba, ya shirya sasanci da su
Gwamnan kudu ya ce IPOB ba su kai 'yan bindiga gurbata ba, ya shirya sasanci da su. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"Dole ne mu tattauna da IPOB. Eh, dole ne mu samu hanyar tattaunawa da su. Wadannan mutanen ba su kai wadanda ke arewa maso gabas ko arewa maso yamma fitina ba. Masu zuwa makarantu kuma su kwashe malamai da dalibai ko kuma su shiga masallaci ko coci su kwashe masu bauta," yace.
"Na yadda cewa akwai wani abu da mutanen nan na yankin kudu maso gabas ke bukata. Akwai wani abu da ya dace a saurara daga wurinsu duk da laifi da ta'addanci ne su dauka makamai.
“Akwai sakon da su ke kokarin aikewa a hakan. Dole ne mu kasance masu karfin guiwa a maimakon amfani da kalaman da basu dace ba a matsayinmu na shugabanni. Najeriya zaune ta ke a kan bam amma kuma hanyar shawo kan matsalar ba ta da wuya."

Kara karanta wannan

Zamfara na fama da 'yan gudun hijira 700,000, gidaje 3,000 sun halaka, Matawalle

Gwamnan Abia ya ce a matsayinsa na gwamnan jihar da Nnamdi Kanu ya fito daga, ya dauke shi a matsayin dan kasa ba wai shugaban kungiyar IPOB ba inda ya kara da cewa ya shirya sasanci da 'yan kungiyar domin samun maslaha, TheCable ta wallafa.

Dakarun sojojin Najeriya sun bindige 'yan awaren IPOB 3

A wani labari na daban, Dakarun sashi na 5 na atisayen Golden Dawn da aka tura Enugu sun sheke mutum 3 da ake zargin 'yan awaren kudu ne da aka fi sani da IPOB, wadanda suka kai wa 'yan sanda farmaki kan babbar hanyar Okija zuwa Onitsha a ranar 7 ga watan Oktoba.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kamar yadda takardar da kakakin dakarun sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu ya fitar tace, zakakuran sojin sun yi artabu da miyagun kuma suka fi karfinsu, lamarin da yasa suka arce.

"Dakarun sojin ba su kakkauta ba suka bi su tare da cigaba da zuba musu ruwan wuta. Uku daga cikin 'yan bindigan da ke tuka motoci biyu kirar Hilux da Hummer bus ne suka bakunci lahira yayin da sauran suka tsere da miyagun raunika."

Kara karanta wannan

Femi Adesina: Ya dace a ce Sanata Abaribe ya na can ya na shakawata a gidan fursuna

Asali: Legit.ng

Online view pixel