'Kona Fasinjoji Da Ransu: Ministan Ƴan Sanda Ya Kare Buhari Kan Ƙin Zuwa Jaje a Sokoto

'Kona Fasinjoji Da Ransu: Ministan Ƴan Sanda Ya Kare Buhari Kan Ƙin Zuwa Jaje a Sokoto

  • Maigari Dingyadi, Ministan Yan Sandan Najeriya ya ce ba zai yiwu Buhari ya iya zuwa jaje ba duk inda aka kai hari saboda yanayin aikinsa
  • Dingyadi ya ce hare-hare da kisa da ake yi sun yi yawa don haka ba zai yiwu Shugaban kasa ya tafi jaje a duk inda aka kai hari ba
  • Bugu da kari, ministan ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya tura tawaga don zuwa jajantawa jihohin Sokoto da Katsina don haka tamkar ya tafi da kansa ne

Ministan Harkokin Yan Sanda, Maigari Dingyadi, ya ce ba zai iya yiwuwa ba Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyarar ta'aziyya jihohi da gidajen wadanda iftila'in rashin tsaro ya shafa ba, Daily Trust ta ruwaito.

A baya-bayan nan dai an yi ta cece-kuce kan rashin kai ziyara da Shugaba Muhammadu Buhari bai yi zuwa jihohin da aka kai manyan hare-hare.

Kara karanta wannan

Na gida ya kashe Dakta Nasir Rabe, Kwamishanan Kimiyar Katsina: Gwamna Masari

'Kona Fasinjoji Da Ransu: Ministan Ƴan Sanda Ya Kare Buhari Kan Ƙin Zuwa Jaje a Sokoto
Ministan Ƴan Sanda Ya Kare Buhari Kan Ƙin Zuwa Jaje a Sokoto. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A makon da ta gabata, zuwa wurin taron kaddamar da littafi da Buhari ya tafi awanni kadan bayan yan bindiga sun kona fasinjoji a Sokoto ya janyo suka gare shi.

Duk da cewa daga bisani, Buhari ya aike da tawaga mai karfi zuwa jihohin Sokoto da Katsina inda munanan harin suka faru, masu sukarsa sun koka kan rashin zuwarsa da kansa.

Dalilin da yasa Buhari ba zai iya zuwa dukkan ta'aziyya da kansa ba

Dingyadi ya ce ba zai yiwu shugaban kasar ya kai ziyara duk inda aka kai hari ba saboda yawaitar kai harin da kashe-kashe da ake yi a baya-bayan nan.

A hirar da ya yi da BBC Hausa, ministan ya ce ba zai yiwu Buhari, a matsayinsa na Shugaban kasa ya kai ziyara dukkan wuraren ba saboda yanayin aikinsa da kuma yawan hare-haren.

Kara karanta wannan

2023: Buhari Ya Yi Hasashen Manyan Abubuwa Da Za Su Faru Zaɓen Shugaban Ƙasa Na Gaba

Ya ce:

"Hare-haren suna faruwa ne kusan a kowanne rana don haka ba zai yiwu ba shugaban kasa ya kai ziyarar ta'aziyya. Kuma idan ka aika tawaga, kamar ka tafi ne da kanka, duk daya ne."

Ministan ya kuma ce jami'an tsaro a kasa suna aiki ba dare ba rana domin dakile hare-haren na 'yan bindigan.

Martanin Dan Majalisar Sokoto

Da ya ke martani a kan batun, dan majalisar jiha mai wakiltar Sabon Birni, Aminu Boza ya ce ba tura tawaga ne abin da suke bukata daga shugaban kasa ba, kawai so suke a kawo karshen hare-haren yan bindiga a jihar.

"Tabbas tawagar shugaban kasa ta zo ta same mu, amma ba abin da muke so ba kenan. Mu mataki muke so a dauka. A karamar hukuma ta, an kashe daruruwan mutane amma gwamnatin tarayya bata dauki mataki ba."

Attahiru Bafarawa, tsohon gwamnan Sokoto, ya yi ikirarin cewa Shugaban kasa bai ziyarci jihar ba saboda rayuwar mutanen ba su da muhimmanci a wurinsa.

Kara karanta wannan

Ba zata saɓu ba, Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan Kwamishina a jihar Katsina

Harin Sokoto: Ina kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiya ta da 'ya'ya na 4 da ransu, Shafa'atu

A baya, kun ji cewa wata mata mai shekaru 30, wacce ta tsira bayan harin da ‘yan bindiga su ka kai wa matafiyan hanyar Kaduna da su ka doshi kudu ta bayyana yadda mahaifiyarta da yaranta 4 su ka kone kurmus, Daily Trust ta ruwaito.

Matar mai suna Shafa’atu, cikin matafiyan ta shaida cewa ita da yaranta, mahaifiyarta, kaninta, da yaran ‘yan uwanta su na cikin motar a wuraren titin Sabon Birni-Isa lokacin da ‘yan bindiga su ka kai musu farmaki.

Shafa’atu, wacce yanzu haka take asibiti inda ake kulawa da lafiyarta sakamakon kunar da ta yi, ta yi hira da manema labarai duk da halin da ta ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164