Mutane 14 sun tsere daga sansanin 'yan bindiga a Sokoto
- Wasu mutane 14 da 'yan bindiga suka sace a Sokoto sun tsere daga sansanin na 'yan bindigan sun dawo gida
- Abubakar Yusuf, shugaban karamar hukumar Isa a Sokoto ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa sun yi farin ciki
- Yusuf ya ce 'yan bindigan sun fita zuwa kai wani harin ne sai wadanda aka tsare din suka samu dama suka tsere suka dawo gida
Jihar Sokoto - Mutane 14 sun tsere daga sansanin 'yan bindiga bayan tsare su da aka yi na kwanaki da wasu yaran hatsabibin dan bindiga Bello Turji suka yi a jihar Sokoto, Premium Times ta ruwaito.
Majiyoyi sun ce mutanen sun tsere ne daga sansanin yan bindiga da ke karamar hukumar Isa a ranar Asabar a yayin da wadanda ke tsare da su suka fita domin kai wasu hare-haren.
Shugaban karamar hukumar ya tabbatar da afkuwar lamarin
Shugaban karamar hukumar Isa, Abubakar Yusuf ya tabbatarwa Premium Times afkuwar hakan a hirar wayar tarho.
Ya ce:
"Eh. An kai su babban asibitin Isa domin a duba su kafin a tura su gida. Mun yi farin ciki ganin suna tsere wa a hankali kuma za mu cigaba da yin addua da bawa sojoji goyon baya don yin nasara kan wannan mutanen."
Mr Yusuf ya ce mutum takwas cikin wadanda suka tsere yan karamar hukumar Sabon Birni ne yayin da uku kuma sun fito ne daga karamar hukumar Isa, duk a jihar Sokoto yayin da sauran ukun 'yan Kauran Namoda ne daga Jihar Zamfara.
Wani dan jarida wanda ya fito daga yankin ya ce wadanda aka sace din sun tsere ne 'a lokacin da yan bindigan suka fita kai hari a wasu kauyuka a yankin'.
Mai magana da yawun yan sandan jihar Sokoto, Sanusi Abubakar, bai amsa kirarsa ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka aike masa ba kan batun.
Harin Sokoto: Ina kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiya ta da 'ya'ya na 4 da ransu, Shafa'atu
A baya, kun ji cewa wata mata mai shekaru 30, wacce ta tsira bayan harin da ‘yan bindiga su ka kai wa matafiyan hanyar Kaduna da su ka doshi kudu ta bayyana yadda mahaifiyarta da yaranta 4 su ka kone kurmus, Daily Trust ta ruwaito.
Matar mai suna Shafa’atu, cikin matafiyan ta shaida cewa ita da yaranta, mahaifiyarta, kaninta, da yaran ‘yan uwanta su na cikin motar a wuraren titin Sabon Birni-Isa lokacin da ‘yan bindiga su ka kai musu farmaki.
Shafa’atu, wacce yanzu haka take asibiti inda ake kulawa da lafiyarta sakamakon kunar da ta yi, ta yi hira da manema labarai duk da halin da ta ke ciki.
Asali: Legit.ng