Innalillahi: 'Yan bindiga sun fito da sabon salo a Zamfara, sun saka sabon haraji
- Mazauna a jihar Zamfara sun bayyana irin halin da suke ciki na yawaitar cutarwa daga 'yan bindiga
- A cewar wasu daga cikinsu, a halin yanzu an saka wa al'umomin yankuna harajin Naira miliyan daya
- Sai dai, a bangare guda, gwamnatin jihar ta ce tana aiki da jami'an tsaro don tabbatar da tsaro a yankunan jihar
Zamfara - ‘Yan bindiga a jihar Zamfara sun fito da sabon salo mai hatsarin gaske yayin da suka bukaci a biya sama da Naira miliyan 1 a matsayin haraji kan yankuna daban-daban a kananan hukumomin Zurmi, Kaura Namoda da Birnin-Magaji na jihar.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da Birnin Tsaba, Gabaken Mesa, Gabaken Dan-Maliki, Turawa, Askawa da Yanbuki, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Mazauna wadannan yankuna an ce yanzu haka suna cikin karkashin ‘yan bindigar da suka kafa gwamnatinsu a yankunan da lamarin ya shafa.
Wani mazaunin daya daga cikin yankunan da ya so a sakaya sunansa, ya ce mutanen Askawa sun biya Naira miliyan 5 kan wasu mutane 18 da aka sace tare da hana kai hare-hare a kan al’ummarsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin da ya ce har yanzu wasu yankuna sun kasa tara kudin har zuwa wa’adin ranar 11 ga watan Disamba da ‘yan bindigan suka bayar, ya ce lamarin ya haifar da firgici a yankunan da lamarin ya shafa.
A cewarsa:
“Yankin Gabaken Mesa ya biya Naira miliyan 1, Gabaken Dan-Maliki Naira miliyan 1 da Birnin Tsaba Naira miliyan 1, ‘yan kadan kenan.”
Ya bayyana cewa an gaya wa yankin Yanbuki su biya Naira miliyan 19 amma ya lura cewa bayan tattaunawa da 'yan bindigan an rage kudin zuwa Naira miliyan 10.
Dangane da ko jama'ar yankunan sun sanar da jami’an tsaro, ya ce:
“Babu wanda zai kai kara ga jami’an tsaro, sanin sarai cewa babu abin da za a yi sai a ce a biya fansa.
“Ni da kaina na je wurin sojoji da yammacin ranar Juma’a a Kaura Namoda domin kai rahoton faruwar lamarin; karshe dai fada nayi da daya daga cikin sojojin. Zan iya gaya muku ba a yi komai ba, har yanzu.”
Gwamnatin Zamfara ta san sarai abin da ke faruwa
A nasa bangaren, kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels wannan mummunan lamari.
Ya ce gwamnatin jihar tana sane da harajin da aka dora wa wadannan al’ummomi amma ya tabbatar da cewa gwamnati na hada kai da jami’an tsaro domin tabbatar da tsaron al’ummomi a yankunan.
A cewer kwamishinan:
“Gwamnati tana aiki tare da jami’an tsaro don tabbatar da cewa wadannan al’ummomin sun samu tsaro."
Sai dai bai bayyana yadda za a kubutar da al’ummomin daga hannun ‘yan bindigan ba, musamman dangane da barnar da ‘yan bindigan ke yi na karbar harajin Naira miliyan daya.
A wani labarin, shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa shi ma ya sha fama da hare-haren ‘yan bindiga da ke addabar arewa.
Ya ce an yi garkuwa da yayansa kuma sai da ya biya kudin fansa domin a sake shi.
Malamin na Kaduna ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Premium Times ta wallafa a ranar Lahadi, 12 ga watan Disamba.
Asali: Legit.ng