Gwamna Zulum ya yiwa sojojin da suka raunata a yaki da ISWAP abin alheri na kudade

Gwamna Zulum ya yiwa sojojin da suka raunata a yaki da ISWAP abin alheri na kudade

  • Sojojin da suka jikkata a wani harin 'yan ISWAP a jihar Borno sun karbi kyautar kudi daga gwamnan jihar, Zulum
  • An ruwaito cewa, gwamnan ya ziyarce su a asibiti, inda ya bada umarnin a raba musu Naira miliyan biyar nan take
  • Ya kuma yaba musu da irin namijin aikin da suke yi, inda ya bayyana su a matsayin masu kishin kasa

Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum ya ziyarci sojojin da suka samu raunuka a wani kazamin fada tsakaninsu 'yan ta'adddan ISWAP a garin Rann da ke kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru a yankin Kala Balge a jihar Borno.

Zulum ya zanta da kuma jajanta wa dukkan sojojin da abin ya shafa a lokacin da ya ziyarce su a asibitin sojoji da ke Barikin Maimalari da ke Maiduguri.

Kara karanta wannan

'Yan IPOB sun dasa bama-bamai, sojoji sun fatattakesu sun kwace tarin makamai

Gwamnan Borno Zulum yayin ziyarar sojoji
Gwamna Zulum ya yiwa wani sojojin da suka raunata a yakar ISAWP goma na arziki | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya samu tarba daga babban kwamandan runduna ta 7 na rundunar soji, Birgediya Janar Abdulwahab Eyitayo, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya bayar da umarnin a bada N5m wanda nan take aka raba wa duk sojojin da ke kwance suna jinya ciki har da wadanda ba su da alaka da yakin Kala-Balge.

Zulum wanda ya samu rakiyar dan majalisar jiha mai wakiltar Kala Balge da kwamishinonin shari’a da na kananan hukumomi da masarautu, ya jajanta wa sojojin, ya yi godiya tare da yaba musu bisa yadda suke nuna kishin kasa.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Brig.-Gen. Onyema Nwachukwu, a wata sanarwa, ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun dora manyan bindigogi da babura tare da kai wa sojojin da aka girke a sansanin ‘Forward Operational Base (FOB)’ da ke Rann hari.

Kara karanta wannan

An tura dakarun Sojoji Najeriya kasar Mali don tabbatar da zaman lafiya

A cewarsa, sojojin sun kashe 'yan ta'adda 26 tare da kwace motocin yakinsu, bindigogin AK47 guda 18 da kuma bindigar M-21 guda daya da dimbin alburusai.

Sojojin sun kuma lalata wasu kayan aikin 'yan ta'addan da dama.

Sojojin sun tilasta wa ‘yan ta’addan yin “watsi da harin nasu, su janye cikin rudani”, duk da cewa “abin takaici, jami’ai biyu da sojoji biyar sun biya mafi tsadar farashi, yayin da jami’ai uku suka samu raunukan harbin bindiga” aka kai su asibiti, inji rahoton This Day.

Luguden jiragen NAF ya yi ajalin kwamandan ISWAP, Abou Sufyan

A wani labarin, shiryayyun luguden da jiragen saman sojojin Najeriya suka yi ya kawo karshen gagararren dan ta'addan kwamandan ISWAP, Abou Sufyan tare da wasu mayakansa a kusa da tafkin Chadi da ke jihar Borno.

PRNigeria tattaro cewa, luguden ruwan wutan da rundunar sojin saman Najeriya ta kaddamar karkashin Operation Hadin Kai ta yi shi ne a ranar Lahadi daidai da wurin da miyagun ke adana makamansu a Kusama da Sigir da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Borno: Mayakan ISWAP sun kashe babban kwamandan sojoji a Rann

Aikin sintiri tare da dubawa da kuma saisatawa da sojojin suka yi, ya bayyana cewa akwai mayakan ta'addancin masu yawa da suka taru a yankin domin shirya kaddamar da farmaki kan sojojin yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.