Nasrun Minallah: Luguden jiragen NAF ya yi ajalin kwamandan ISWAP, Abou Sufyan

Nasrun Minallah: Luguden jiragen NAF ya yi ajalin kwamandan ISWAP, Abou Sufyan

  • Gagarumin luguden wuta da sojin saman Najeriya suka yi wa 'yan ta'addan ISWAP a yankin tafkin Chadi ya yi ajalin sabon kwamandansu, Abou Sufyan da mukarrabansa
  • Sojojin saman sun yi amfani da jirgin ATF Super Tucano inda suka kai farmaki kan mayakan ISWAP da ke shirya yadda za su kai farmaki kan sojojin Najeriya
  • Kamar yadda majiyar sirri ta tsaro ta sanar, sojin saman sun yi ruwan wutan ne a kan ma'adanar makamai, fetur da ababen hawan 'yan ta'adda

Shiryayyun luguden da jiragen saman sojojin Najeriya suka yi ya kawo karshen gagararren dan ta'addan kwamandan ISWAP, Abou Sufyan tare da wasu mayakansa a kusa da tafkin Chadi da ke jihar Borno.

PRNigeria tattaro cewa, luguden ruwan wutan da rundunar sojin saman Najeriya ta kaddamar karkashin Operation Hadin Kai ta yi shi ne a ranar Lahadi daidai da wurin da miyagun ke adana makamansu a Kusama da Sigir da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yiwa sojojin da suka raunata a yaki da ISWAP abin alheri na kudade

Nasrun Minallah: Luguden jiragen NAF ya yi ajalin kwamandan ISWAP, Abou Sufyan
Nasrun Minallah: Luguden jiragen NAF ya yi ajalin kwamandan ISWAP, Abou Sufyan. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Aikin sintiri tare da dubawa da kuma saisaitawa da sojojin suka yi, ya bayyana cewa akwai mayakan ta'addancin masu yawa da suka taru a yankin domin shirya kaddamar da farmaki kan sojojin yankin.

Wata majiyar sirri ta sanar da PRNigeria cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Jirgin ATF na Super Tucano a yayin kai farmaki a yankin, ya saki ruwan wuta mai yawa wanda kai tsaye ya samu ma'adana da wurin sarrafa makaman 'yan ta'addan, ma'adanar man fetur da sauran ababen bukata na motoci da babura.
“Wasu daga cikin 'yan ta'addan sun nemi tserewa daga yankin amma an tare su tare da halaka su a farmakin bin bayan da sojojin Najeriya suka yi.
"Wannan luguden na mako daya da aka dinga yi wa 'yan ta'addan ya taka rawar gani wurin hargitsa mayakan ta'addanci tare da tada hankalin kungiyar da kuma lalata shirinsu na kai wa sojoji farmaki.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Tsagerun yan bindiga sun sake tasa keyar dandazon mutane a jihar Kaduna

"Mun san da wasu daga cikin 'yan ta'addan sun samu sun tsira da ransu yayin da wasu suka samu raunika sannan suka tsere cikin bishiyoyin Arinna Sorro da Arinna Ciki."

ISWAP sun saci fasinjoji 15 a Borno, sun iza keyarsu cikin dajin Sambisa

A wani labari na daban, a kalla fasinjoji 15 ne miyagun da ake zargin mayakan ta'addancin ISWAP ne suka sace a Borno.

Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa, an sace jama'ar ne a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Majiyar ta ce 'yan ta'addan sun kai farmaki ne wurin kauyen Gumsuri da ke karamar hukumar Damboa ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel