Borno: Mayakan ISWAP sun kashe babban kwamandan sojoji a Rann

Borno: Mayakan ISWAP sun kashe babban kwamandan sojoji a Rann

  • Ana fargabar mayakan ISWAP sun halaka daya daga cikin kwamandojin wata bataliya ta Operation Hadin Kai tare da wasu sojoji biyar
  • Ana zargin mummunan lamarin ya auku ne a Rann, wani gari da ke karkashin karamar humumar Kala Balge da ke jihar Borno a ranar Alhamis
  • An samu rahotanni akan musayar wutar da ta shiga tsakanin mayakan da kuma sojojin wanda su ka kwashe sa’o’i da dama su na yi

Jihar Borno - Ana zargin mayakan ISWAP sun halaka daya daga cikin kwamandojin bataliyoyi daga rundunar Operation Hadin Kai, kamar yadda wata majiya ta sanar da The Cable.

Ana zargin sun halaka babban sojan tare da wasu sojoji biyar bayan sun kai farmaki Rann, wani gari da ke karkashin karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Na janyo wa jama'ar Yesu abin kunya: Faston da aka kama ya yi garkuwa da Faston Katolika

Borno: Ana fargabar mayakan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Rann
Ana kyautata zaton 'yan ta'addan ISWAP sun halaka babban soja a Borno. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

An samu bayanai akan yadda musayar wuta ta auku tsakanin sojojin da mayakan na tsawon sa’o’i.

Sojoji ma sun halaka 20 cikin mayakan

The Cable ta ruwaito yadda sojojin su ka halaka mayakan ISWAP 20 yayin musayar wutar.

Ba a samu Kakakin rundunar sojin, Onyema Nwachukwu ba don jin tsokacinsa akan harin.

Lamarin ya auku ne bayan makwanni uku da mayakan ISWAP su ka halaka Dzarma Zirkusu, birgediya janar kuma kwamandan army birged na Chibok.

Zirkusu ya na hanyarsa ta zuwa Askira don samun tallafi ga rundunoni inda su ka dana masa tarko su ka halaka shi.

An halaka janar din tare da wasu sojoji uku

A cikin takardar, Onyema ya shaida cewa:

“Sai dai abin takaicin shi ne yadda muka rasa birgediya janar Dzarma Zirkusu da wasu sojoji yayin da su ke kokarin yakar ‘yan ta’adda da kare yankunansu.”

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke dan IPOB yayin da tsagerun ke kokarin sace likitoci a jihar Imo

Borno: Hotunan ragargazar da sojoji suka yi wa ISWAP a Askira Uba, sun kashe 50 sun kwato makamai

A wani labarin mai alaka da wannan, Rundunar Operation Hadin Kai ta Sojoin Nigeria da ke arewa maso gabas ta samu nasarar halaka mayakan ISWAP guda 50 a karamar hukumar Askira Uba.

Hedkwatar tsaron Najeriya ta shafin su na Facebook sun bayyana yadda sojojin su ka yi gaba da gaba da mayakan ISWAP wanda har lalata mu su kayan yakin su suka yi.

Lamarin ya auku ne a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba inda jaruman sojin suka samu nasarar halaka manya da kananun mayakan kungiyar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel