Wani mutum ya kashe mai sayar da sigari da duka saboda N50 kacal
- Wani bawan Allah mai suna Mukaila Adamu ya riga mu gidan gaskiya kan canji ta N50 kacal a Idiroko a Legas
- Wani Biodun Adebiyi ne ya siya sigari wurinsa ya dawo karbar canjin N50 kwatsam sai rikici ya barke tsakaninsu
- Mahaifin Mukaila ya ce yayin rikicin ne Adebiyi ya yi wa dansa naushi daga nan ya yanke jiki ya fadi
Ogun - Yan sanda a jihar Ogun sun kama wani mutum mai shekar 32, Biodun Adebiyi, kan yi wa wani mai sayar da sigari dukar da ya yi sanadin rasuwarsa saboda Naira 50 kacal.
Premium Times ta ruwaito cewa mai magana da yawun yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin.
A cewar yan sandan, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a yankin Ajegunle na Idiroko inda marigayin, Mukaila Adamu, mai shekaru 30, ke sayar da sigari a shagon mahaifinsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rikici kan canjin N50 ya yi sanadin rasuwar Mukaila
Jaridar ta rahoto cewa wanda ake zargin ya yi wa Adamu duka har ya mutu ne saboda ya ki bashi canjinsa na Naira 50.
Cikin sanarwa, yan sandan sun ce:
"An kama wanda ake zargin ne a ranar 5 ga watan Disamban 2021, bayan rahoto da mahaifin marigayin, wani Adamu Abubakar ya shigar a hedkwatar yan sanda ta Idiroko ya ce wanda ake zargin ya zo shagonsa a Ajegunle misalin karfe 2 na rana ya siya sigari kuma dansa Munkaila Adamu ya sayar masa.
"Ya kara da cewa misalin karfe 10 na dare, wanda ake zargin ya dawo ya bukac a bashi canjinsa N50. Hakan ya janyo rikici tsakaninsa da dansa, ana hakan ya yi wa dansa, Mukail Adamu, naushi, nan take ya fadi kasa, aka garzaya da shi asibiti aka tabbatar ya mutu."
An kama wanda ake zargin an kuma fara bincike
Mr Oyeyemi ya ce bayan an shigar da rahoton, DPO na Idiroko, Shadrach Oriloye, ya tura jami'ansa su tafi wurin da abin ya faru inda aka kama wanda ake zargin.
"An kai gawar marigayin asibiti inda za a yi gwaji don sanin sanadin mutuwarsa," in ji Mr Oyeyemi.
Kwamishinan yan sandan Jihar Legas, Lanre Bankole, ya umurci a tura wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka wato SCID don zurfafa bincike.
'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe
A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.
Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.
Asali: Legit.ng