Da duminsa: Bayan wata 1 hannun yan bindiga, an saki Kiristoci masu bauta 60 da aka sace a Coci

Da duminsa: Bayan wata 1 hannun yan bindiga, an saki Kiristoci masu bauta 60 da aka sace a Coci

  • Bayan kimanin kwanaki 35 hannun tsagerun yan bindiga, an saki masu bauta a cocin Bantis na Kaduna
  • Masu bautan na tsakiyar ibada ranar 31 ga Oktoba yan bindiga suka kai musu farmaki sukayi awon gaba da su
  • Wani dan'uwan wadanda aka sace wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa an biya kudin fansa

Kaduna - Mambobin Cocin Emmanuel Baptist dake Kakau Daji a jihar Kaduna kimanin mutum 60 sun shaki kamshin yanci bayan sama da wata guda hannun tsagerun an bindiga.

Daily Trust ta ruwaito cewa Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya CAN, reshen Kaduna, Rabara Joseph John Hayab, ya tabbatar da hakan ranar Asabar.

A cewarsa, sabanin mutum 60 an saki wasu mutane tara da aka sace a wani kauye da yammacin Juma'a, 3 ga Disamba, 2021.

Kara karanta wannan

Dalibin SS3 ya doki Malami har lahira saboda ya zane kanwarsa

Rahoton yace Rabaran John bai yi magana kan kudin fansan da aka biya ba.

A cewarsa:

"Lallai an saki mambobin Cocin Kakau Daji da daren jiya kuma Cocin ya bayyana cewa sun taka rawar gani kuma na jinjina musu."

Daily Trust tace wani dan'uwan wadanda aka sace wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa an biya kudin fansa.

Kiristoci masu bauta 60 da aka sace a Coci
Da duminsa: Bayan wata 1 hannun yan bindiga, an saki Kiristoci masu bauta 60 da aka sace a Coci Hoto: Coci
Asali: Facebook

Barayin da suka sace masu ibada sama da 60 a Kaduna sun bukaci Buhunan shinkafa da jarkan mai

A baya mun kawo muku cewa maharan sun buƙaci buhunan shinkafa da jarkan man gyada domin ciyar da mutanen.

Rahotanni sun bayyana cewa ɓarayin sun yi barazanar cewa matukar ba'a gaggauta kai musu kayan abincin nan ba to zasu bar mutanen cikin yunwa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake DPO na yan sandan da aka sace bayan kwanaki 6 hannunsu

Shugaban ƙungiyar kiristoci (CAN) reshen jihar Kaduna, John Hayab, ya shaida wa manema labarai cewa ɓarayin suna neman a basu maƙudan kuɗaɗe.

A kalla mutane 60 ‘yan bindiga su ka sace a cocin Emmanuel Baptist da ke Kakau Daji a karamar hukumar Chikun a jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

‘Yan bindigan sun isa cocin dauke da miyagun makamai inda su ka fara harbe-harbe ko ta ina ana tsaka da bautar ranar Lahadi, 31 ga Oktoba, 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng